✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu iya fara fitar da shinkafa badi – Kungiyar RIFAN

Aminiya: Yaya kuke gudanar da rabon bashin noman shinkafa na bana? Shugaban RIFAN: Lura da makudan kudin da gwamnati ke kashewa don shigo da shinkafa…

Aminiya: Yaya kuke gudanar da rabon bashin noman shinkafa na bana?

Shugaban RIFAN: Lura da makudan kudin da gwamnati ke kashewa don shigo da shinkafa cikin kasar nan, inda alkaluma suka nuna ana kashe samar da Naira tiliyan a kan haka, don magance wannan sai Gwamnatin Tarayya ta karkata hankalinta ga noman shinkafa tare da karfafa gwiwar manoma a kan noman shinkafa. Hakan ya sa gwamnatin ta bullo da shirin bayar da bashin noman shinkafa na Anchor Borrowers inda ta damka gudanar da shi ga Babban Bankin Najeriya (CBN) inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a shekarar  2015 a Jihar Kebbi.

A shekarar 2016 muka gudanar da shi a Jihar Kano tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar. Kasancewar an samu matsalar rashin biyan bashin a wanacan lokaci gwamnatin jihar ta cire hannunta. Don haka a matsayinmu na kungiya a shekarar 2017 muka shige gaba muka karbo bashin ba tare da sa hannun gwamnati ba, inda aka ba mu Naira biliyan takwas.

To a bana ma mun sake karbo wannan bashi, a watannin baya mun  raba irin wadannan kaya ga manoman rani dubu 25 inda aka kashe Naira biliyan shida a yanzu kuma muna rabawa don noman damina wanda kudin ya kusan Naira biliyan 45.

Aminiya: Me kuke bayarwa ga manoman ke nan?

Shugaban RIFAN: Abin da muke bayarwa shi ne kayan aiki ba kudi ba, shi kuma manomi zai biya bashin da shinkafar da ya noma, a wannan harka gaba daya ba gilmawar kudi a tsakanin mai bayar da bashi da mai biyan bashi. Manomin da ke da gona mai fadin kadada daya muna ba shi Naira dubu 219 shi kuma manomi zai bayar da shinakafa buhu 22. Lissafin ya fara tun daga kan gyaran gona har zuwa kan buhunan da za a zuba shinkafar bayan girbi yana ciki. Za a ba shi buhun taki shida, shi kuma iri za a samu kilo talatin, za a ba ka maganin feshi lita shida sai kuma injin ban- ruwa mai inci uku, sai dai a wannan lokaci mun samu karancin injin ban-ruwa don haka mai inci biyu gare mu a yanzu, wanda kuma mun san ba kudinsu daya da mai inci uku ba. Saboda haka idan mutum ya tashi biyan bashinsa dole za a rage masa yawan buhunan shinkafar da zai bayar a matsayin biyan bashi.

Wani abin burgewa da wannan shiri shi ne ba a lokaci guda manomi zai biya ba. Manomi zai biya kashi uku, wato zai bayar da buhu takwas da noman daminar bana, sannan ya sake juya kudin ya yi noman rani idan ya yi girba zai bayar da buhu bakwai sannan zai sake juya kudin ya yi noman wata daminar shi ma ya bayar da buhu bakwai. Manomin da ba a yi masa gyaran gona da girbi ba, shi kuma zai biya buhuna.

Aminiya: Manoman da ke karbar wadannan kayayyaki sun yi korafin rashin samun cikakkun kayan da ka lissafa a sama  inda suka gwammace da tsabar kudi aka ba su maimakon kayan. Me ya jawo haka?

Shugaban RIFAN: Kasancewar aikin mun raba shi ga kananan  hukumomi, mun kuma gaya wa manoma cewa duk wanda kayansa ba su cika ba, to ya koma wurin jami’anmu na kananna hukumomi su yi musu korafi, idan kuma har ba su ba, to su zo su gaya mana za mu dauki matakin da ya dace. Su kuma masu cewa a ba su tsabar kudi, wadannan ba manoman gaskiya ba ne, domin in dai mutum noman zai yi da gaske, idan an ba shi kudin ma kayan zai je ya saya. To ga shi an ba ka kaya, ai ina ganin an hutar da kai. Dama kin san wadansu ba manoma ba ne manema ne.

Aminiya: Wane tsari kuka yi a wannan karon wajen tabbatar da manoma sun mayar da bashin da suka karba lura da irin abin da ya faru a shekarun baya inda manoman suka ki biyan bashin?

Shugaban RIFAN: A gaskiya mun yi tsari mai kyau a kan haka domin mun nuna kowa sai yana da wanda zai tsaya masa, don haka muna da lauyoyinmu da ke tsaye a kan harkar inda muke fatan ba za a sake maimaita abin da ya faru a baya ba. Shi ma wancan bashin da ya makale a wurin manoma kungiya tana nan tana bibiyar manoman da suka karba don ganin sun dawo da shi, duk da cewa akwai kwamitin gwamnati na Farfesa Mahmud wanda yake kokarin karbo bashin kuma har mutane sun fara biya jefi-jefi.

Aminiya: Gwamnatin Tarayya na fatan ganin an daina shigo da shinkafa gaba daya waje, a koma cin shinkafar gida, kana ganin za ku iya samar da shinkafar da za ta wadaci Najeriya?

Shugaban RIFAN: kwarai da gaske domin a yanzu manoman shinkafa mun yi nisa wajen noma shinkafar. Muna hangen nan da shekara daya zuwa biyu za mu fara fitar da shinkafa zuwa wasu kasahen waje ba kawai batun ciyar da ’yan kasarmu ba, saboda yadda manoma suka raja’a a kan noman shinkafa.

Wani abin farin ciki kuma shi ne an samu kwarewa wajen gyaran shinkafar yadda take gogayya da ta kasashen waje. A yanzu haka  duk kasuwar da kika je za ki ga shinkafarmu ce ta gida da ake sayarwa, yanzu fa ta kai cewa mutane suna sayen shinkafar gida ba tare da sun san ita ba ce saboda kyawun shinkafar.

Aminiya: Wane kira gare ka ga manoman?

Shugaban RIFAN: Ina kira gare mu da mu sa kishi a cikin abin da muke yi. Allah Ya albarkaci kasarmu da kasar noma mai kyau, ga kuma gwamnati ta yi hobbasa wajen tallafa mana. Don haka abin da ya rage shi ne mu rike harkar nan da gaskiya. Idan muka yi haka arzikin kasarmu zai dawo gare mu maimakon daukarsa da ake yi ana kaiwa wasu kasashe wajen shigo mana da abinci kasarmu. Har ila yau hakan zai sa kasarmu ta bunkasa al’ummarmu su samu aikin yi.

Sannan muna kira ga wadanda suka karbi kayan tallafin nan a lokacin noman rani. Lokaci ya yi da za su dawo da bashin, ma’ana shinkafar da suka noma. kofa a bude take su je kananan hukumominsu inda suka yi rajista su biya sannan su karbi rasidansu. Mu sani cewa shi fa samun tallafin bashin nan arziki ne domin a wasu lokuta mutum yana son yin noman idan ba ya da kudi ko bashi da mai ba shi bashin sai dai ya hakura ya noma daidai kudinsa. Me ya sa kuma mun karba mun yi amfani da shi sun taimaka mana mun samu amfanin gona kuma mu kasa dawo da shi don wadansu ’yan uwanmu su amfana ko kuma mu da kanmu mu sake amfana? Tsarin tallafin ya ba manomi damar idan ya gama biyan bashinsa zai iya sake karbar wani bashin idan yana bukata.