✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu magance ainihin dalilin rikicin matasa —Gwamnoni

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi ittifakin rage zaman banza tsakanin da rikicin matasa a dukkannin jihohi. Gwamnonin sun yi amannar cewa rashin daidaito ta…

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi ittifakin rage zaman banza tsakanin da rikicin matasa a dukkannin jihohi.

Gwamnonin sun yi amannar cewa rashin daidaito ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa ne musabbabin rigingimun matasa a sassan Najeriya.

Don haka suka yanke shawarar magance matsalar a matakan jiha da shiyyoyin siyasa ta hanyar bin tsare-tsaren da Karamin Kwamitin Tattaunawa na Majalisar Tattalin Arziki na Kasa ya fitar.

Taron Gwamnonin na ranar Laraba ya yi ittifakin zai tattauna da sarakuna, shugabanni da kungiyoyin addinai da na kare hakki domin cimma nasara a manufar.

NGF ta ce tattaunawar gwamnonin da masu ruwa da tsaki zai kuma mayar da hankali domin ganin yadda jama’a za su rika bayar da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro.

Da yake karin haske game da abin da zanga-zangar #EndSARS ta haifar, Shugaban kungiyar, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya nanata muhimmancin da gwamnoni suka ba wa batun tsaro.

Ya kuma yaba da karin haske da gammayar masu yaki da annobar coronavirus (CACOVID19) ta yi kan abin da ya kira “gurguwar fahimtar da dabaibaye sha’anin rabon kayan tallafin a jihohi”.