Kwamitin kula da harkokin jiragen kasa da gwamnatin tarayya ta nada domin inganta sufurin jirgin kasa, karkashin shugabancin Alhaji Abubakar Kawu Baraje, ya kai ziyarar gani da ido a tashar jirgin kasa da ke Ikko, inda ya ce zai nemi gwamnatin ta kara kudi a bangaren sufurin.
Sa’ilin da yake zagayawa, shugaban kwamitin ya ce kodayake gwamnati na hasarar kudi a wannan wurin, amma nan ba da jimawa ba duk zai zame tarihi saboda tattaunawar da kwamitin zai yi da ministan sufuri da shugabannin hukumar da kuma shugaban kasa don inganta harkokin jirgin kasan.
Ya ce mayar da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya, zai talmaka wa talaka, saboda saukinsa da kuma raguwar hatsari.
Dangane da tsoffin kayayyaki, Alhaji Baraje ya ce hukumar za ta jingine su ta rungumi na zamani, duk dayake suna da sauran amfani.
Daga cikin injiniyoyin da ya zagaya da kwamitin, Injiniya Zayyana Kabir ya yi nunin komai tsufan jirgi ana iya gyara shi muddin dai za a samu wadatattu kayan aiki, daya daga cikin manya-manyan matsalolin da ke addabarsu, amma muddin za su samu, ba wani taragon da zai gagari gyarawa a dakin gyare-gyare da ke Ikko da Enugu da Zaria da Minna.
Yanzu dai jirgin kasa ya fara aiki daga Legas zuwa Kano sau biyu a sati.
Za mu yi kokarin ganin an inganta sufurin jiragen kasa
Kwamitin kula da harkokin jiragen kasa da gwamnatin tarayya ta nada domin inganta sufurin jirgin kasa, karkashin shugabancin Alhaji Abubakar Kawu Baraje, ya kai ziyarar …