✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: Buhari talakawa suka yi ba Jam’iyyar APC ba – Adamu Katagum

Shugaban Gidauniyar Talakawa Alhaji Adamu Umar Katagum ya ce talakawa sun zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne a zaben Shugaban Kasa da ya gabata ba…

Shugaban Gidauniyar Talakawa Alhaji Adamu Umar Katagum ya ce talakawa sun zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne a zaben Shugaban Kasa da ya gabata ba jam’iyya suka zaba. Alhaji Adamu Katagum ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce yi talakawa sun zabi cancanta ne, lamarin da ya sanya Shugaba Buhari ya yi nasara da rinjaye mai girma a jihohin Arewa.                                                                                                                                                  “Amma lokacin zaben gwamnoni sai ga Jami’yyar PDP ta yi nasara a wasu jihohin Arewa kamar Bauchi da Sakkwato inda APC ta sha da kyar a Jihar Kano, wannan alamu ne da suke tabbatar da gogewar talaka a siyasance domin yanzu ba maganar jam’iyya ake yi ba, talakawa sun yi wayewar da idan ba ka tabuka musu abin arziki ba, za su kayar da kai da karfin kuri’arsu ko da kuwa nawa za ka kashe, kuma komai karfin mulkinka,” inji shi.                                                                                                                                                     Ya kara da cewa: “Wannan shi ne ya faru a jiharmu ta Bauchi don haka wannan izina ce ga gwamnonin da sauran zababbun ’yan siyasa a matakai daban-daban, don haka wajibi ne su yi wa talakawa aiki in kuma sun ki akwai ranar kin dillanci.”

Ya ce lokaci ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari zai waiwayi talakawa a sabuwar gwamnatin da zai kafa domin talakawa sun yi masa adalci fiye da yadda ba a zato, “Fatarmu ita ce talakawa su amfana kuma wadanda suka yi fadi ta shi a wannan tafiya a saka musu,” inji Adamu Katagum.

Sai ya yi kira ga ’yan Nigeriya su ci gaba da yi wa Shugaba Muhammadu Buhari addu’a domin cimma nasara a al’amuran da ya sanya a gaba na gina kasar nan.