✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: ’Yan fim sun rabu kan Buhari da Atiku

A wani bincike da Aminiya ta gudanar ta gano masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood ta rabu biyu kan ’yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar…

A wani bincike da Aminiya ta gudanar ta gano masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood ta rabu biyu kan ’yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari da kuma dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Binciken Aminiya ya gano kungiyoyin da suka raba kan ’yan fim din sun hada da All Progressibes Congress (APC) Northern Musicians Forum (ANMFO) da ke goyon bayan Buhari da kuma Kannywood Initiatibe Door-2-Door for Atiku 2019 da ke goyon bayan Atiku.

Binciken ya nuna ’yan fim din da ke goyon bayan Atiku sun hada da Mika’il Bin Hassan (Gidigo) da Sani Danja da Fati Muhammad da Zaharaddeen Sani da Usman Mu’azu da Ummi Zee-Zee da Salisu Mu’azu da Mustapha Naburuska da mawaki Abubakar Sani da sauransu.

’Yan kungiyar ANMFO da ke goyon bayan Buhari sun hada da mawaki Dauda Kahutu Rarara da Yusuf Haruna (Baban Chinedu) da Adam A. Zango da Bello Muhammad Bello da Fati Nijar da Abdul Amart (Mai Kwashewa) da Halima Atete da Jamila Nagudu da Aminu Ladan Abubakar (ALA) da Rukayya Dawayya da sauransu.

’Yan kungiyar Kannywood Initiatibe Door-2-Door for Atiku 2019 sun bayyana cewa suna goyon bayan Atiku ne saboda kwarewarsa kan tattalin arziki, sannan Buhari ya gaza inda ya jefa al’ummar Najeriya cikin mawuyacin hali.

’Yan kungiyar ANMFO kuwa sun ce suna goyon Buhari ne saboda sun gamsu da salon mulkinsa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro, yaki da cikin hanci da rashawa da kuma yin ayyukan ci gaba da kuma raya kasa.

Kodineta na kasa na kungiyar Kannywood Initiatibe Door-2-Door for Atiku 2019, Mika’il Isah Bin Hassan ya ce abin da ya ja hankalinsu har suka kafa wannan kungiya shi ne, don samar wa ’yan kasa mafita, kuma saboda Buhari ya  nuna wa ’yan fim halin ko in kula, duk da wahaltawar da suka yi masa a baya, inda har yanzu babu wani abu na ci gaba da suka samu.

Ya ce, “Sana’armu ta gurgunce, kasuwa ta mutu, wannan ta sa muka nemo wa kanmu mafita, domin Wazirin Adamawa, yana da tsari na samar da ayyukan yi da kuma inganta kasuwanci a kasar nan, don haka ya kamata mu mara masa baya, don a fita daga cikin kuncin da ake ciki na rashin tabbas a kan harkokin tattalin arziki da rashin tabbas a kan halin matsi.”

Mika’il wanda a harkar fim aka fi sani da ‘Gidigo’ ya bayyana cewa sun fara wannan tafiya ne tun daga lokacin da aka fara batun fitar da dan takara na jam’iyyu, kuma kama yanzu a kowace jiha suna da kodinetoci da kuma masu taimaka musu mutum takwas.

“Sannan kowace karamar hukuma akwai shugabanni, sannan akwai kwamiti-kwamiti, akalla dai muna da mutanen da suke shugabanci da kuma na kwamiti-kwamiti sama da mutum dubu 300, kungiya ce da take wakiltar Arewacin Najeriya, ta kuma shafi ’yan fim da mawaka da makada na zamani da na gargajiya,” inji shi.

Ya ce fitattun ’yan fim da ke cikin tafiyar sun hada da, Sani Danja da Ummi Zee-Zee da Zaharaddeen Sani da Fati Lamaj da mawaki Abubakar Sani da Al’Amin Ciroma da Salisu Mu’azu da Usman Mu’azu da Hafizu Bello da Mustapha Naburaska da sauransu.

Ya bayyana cewa dangane da hanyoyin da za su bi wajen tallata Atiku sun hada da amfani da kafar sadarwa irinsu Facebook da Twitter da Instagram, sannan za su rika bin kauyaka don tallata Atiku, za su bi mutane har gidajensu don tallata musu Atiku.

Ya ce ba za su yi kamfen da cin mutunci ba, sannan za su tallata Atiku da gamsassun hujjoji don har a kai ga cewa Atiku ya lashe zaben 2019.

Ya ce, “Masu magana da cewa duk ’yan Kannywood na goyo bayan Buhari duk karya ne, domin daruruwan ’yan fim suna goyon bayan Atiku, don haka ba duk ’yan Kannywood suke goyon baya Buhari ba.”

Gidigo ya caccaki masu ganin baiken Atiku don ya canza sheka daga APC zuwa PDP.

Ya ce, “Tambayoyi zan yi ga ’yan Najeriya, a 2014 Shugaba Buhari da kuma Atiku tare suka yi gwagwarmaya, Atiku ya bayar da gudunmuwa har Buhari ya zama shugaban kasa a 2015, a wancan lokacin Atiku gwarzo ne, Atiku yana APC gwarzo ne ba barawo ba, amma yanzu da ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP to shi barawo ne, ina shaida?”

“Don haka kada ’yan Najeriya su yarda da rudu.  Idan har Atiku zai kafa kamfanoni don ’yan kasa su ci gaba, to idan aka ba shi shugabancin kasa zai samar da ayyukan yi. An ce a yi noma, yanzu ana noma me ya sa lokacin da ba a noma abincin ya fi araha?” Ya jaddada tambayarsa.

Sai dai a nasa jawabin, Shugaban riko na Kungiyar mawaka mai suna APC All Progressibes Congress (APC) Northern Musicians Forum (ANMFO), Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu ya ce dalilin gamsuwarsu da salon mulkin Buhari ya sa suka ci gaba da yi masa kamfe don ya lashe zaben 2019.

Ya ce, ya kamata a yaba wa Buhari saboda, “Buhari ya karbi wannan kasa a tabarbare, ku ’yan jarida ne da mu da sauran jama’a mun san ya karbi kasar nan a rushe, abin da ya rage mata kadan ne, kasashen duniya sun yi hasashen ko ma waye ya karbi Najeriya to ba zai iya tattale ta ta dawo kan mazauni daya ba, amma haka Allah Ya ba Buhari ikon dawo da martabar kasar nan a idon duniya, duk da ya fado cikin makiya, mutanen da ba kasar ce a gabansu ba.”

Ya ce, idan har da kwadayin duniya ko kudi suke yi, to ba za su yi Buhari ba, “saboda an nuna mana duniya, a cikin duk wadanda suka nemi shugabancin kasar nan babu wanda bai fi Buhari abin duniya ba, amma sun sani, mun sani babu Allah a ransu, ba kasar nan a ransu, shi ya sa muka goyi bayan Buhari saboda yadda yake so a gyara kasar nan.”

Baban Chinedu ya caccaki majalisa karkashin shugabacin Bukola Saraki inda ya ga baikensu kan yadda suke kin yin abin da ya dace idan an kai musu kasafin kudi.

“Abin takaici ne yadda idan aka tura kasafin kudin Najeriya don a yi aiki sai su rike shi, su ki yin abin da ya dace, duk da rashin kudi, amma Buhari ya saita kasar nan.” Inji shi.

Dan gane da batun cewa babu dan fim da ya amfana da gwamnatin Buhari, sai ya ce, “ba gaskiya ba ne, domin babu wanda ya kai dan fim zuwa taro, indai a shiga taro a nemi kudi ne, to babu sama da dan fim, amma a shekarun baya an kai lokacin da za a kira dan fim ya ki zuwa wajen taro, saboda idan ya je to yana tunanin bam zai iya tashi a wurin. Amma yanzu kowa yana iya shiga taro gaba gadi, ka je taro ka fito wannan yana daga cikin albarkar da ya jawo wa ’yan fim.”

Ya ce, kungiyarsu za yi kokari wajen fadakar da mutane don su fahimci inda gwamnatin Buhari ta dosa, domin ba a taba yin gwamnatin da ake ci mata dunduniya kamar gwamnatin Buhari ba, idan aka tara manyan kasar nan 100, to 99 suna yakar wannan gwamnatin, saboda Buhari ya hana harambar din da suke yi.

Ya bukaci mutane su ci gaba da ba Buhari goyon baya, domin a yanzu ya tara kudi, sannan idan ya dawo karo na biyu zai yi ayyukan ci gaba da ba a taba yinsu a tarihi ba.

Ya ce, “Idan gwamnatin PDP ta ce ta yi ayyuka, sannan ba ta ga ayyukan da Shugaba Buhari ya yi ba, to ita ayyukan da ta dauko irin su tagwayen hanyoyi daga Kano zuwa Maiduguri, daga lokacin da aka ba da kwangilar yau shekara kusan 16 ke nan, duk shekarar duniya a kasafin kudin sai an fitar da kudin, a wannan shekarun ko guragu ne ke yin hanyar ya kamata a ce an kare ta, amma zuwan Buhari ya biya bashin biliyoyin Naira ga kamfanonin da ke yin hanyoyi a kasar, kafin yanzu da aka ci gaba da yin ayyukan hanyoyi a kasar nan.”

Baban Chinedu ya kara da cewa akwai titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna wacce gwamnatin PDP ce ta fara yi a kan Dala biliyan 50, amma ba ta kawo jirgin ba, ba ta kuma yi tashar jirgin ba, amma zuwan Buhari aka karasa aikin.

Ya ce, “Ga aikin tashar wutar lantarki ta Shiroro, an fitar da kudi lokacin mulkin PDP, amma aka cinye kudin, inda yanzu gwamnatin Buhari ta ci gaba da yin aikin. A lissafin da muka yi kwanaki mun gano cewa Buhari ya ci gaba da yin ayyukan da PDP ta faro sama da 360.

…Masana sun yi sharhi

A lokacin da Aminiya ta tuntubi mai sharhi kan al’amuran da suka shafi Kannywood, Muhsin Ibrahim sai ya ce hakan abin murna ne idan aka yi la’akari cewa a shekarun baya ’yan fim ba su samu damar ganawa da wani shugaban kasa ko dan takarar shugabancin kasa ba.

Muhsin wanda Malami ne a Jami’ar Cologne da ke kasar Jamus, ya ce, “A yanzu ’yan Kannywood sun ziyarci Shugaba Buhari kusan sau biyu a ’yan watannin nan, na kalli kuma bidiyon da wasu ’yan fim suke yi wa Atiku Abubakar kamfen, hakan abu ne mai kyau, musamman ma idan aka yi la’akari a baya ’yan fim ba sa samun damar ganawa da shugaban kasa. Zan iya tunawa a baya idan ka cire Sani Danja babu wani dan fim da yake iya ganin Shugaban Kasa.”

Ya ce, ya san wadansu za su yi tunanin yin amfani da ’yan fim wajen yin kamfen ba zai taka wata rawa wajen zabe ba, to amfanin ’yan fim zai taka muhimmiyar rawa a zaben 2019.

Ya ce, “Kowa ya san ’yan fim suna da farin jini, kuma suna da tasiri wajen canza ra’ayin mutane, a yau jarumai da mawaka sun fi ’yan siyasa da shugabanni yawan mabiya a kafafen sadarwa na zamani, wadansu mabiyan ’yan fim kamar bauta musu suke yi, don haka za su iya zaben ko ma waye ’yan fim suka nuna suna tare da shi.”

Ya ce shawarar da zai ba ’yan Kannywood ita ce su yi amfani da wannan damar su nemi wani abu mai girma da muhimmanci da zai taimaki masana’antarsu.

“Na san abu ne mai wahala a dawo da batun gina alkaryar daukar fim, amma akwai matsaloli masu yawa da suka addabi Kannywood, amma ban ji suna magana a kansu ba, ka san mutane da yawa sun fi damuwa da kansu ne, damuwar mutane shi ne sha yanzu magani yanzu, ba sa tunanin tanadin gaba ko shiri don gaba ba.”

Muhsin ya bukaci kada ’yan fim su bari bambancin siyasa ya raba kansu, domin hakan zai iya rusa Kannywood.

Ya ce, “Kada ’yan fim su bari bambancin siyasa ya sa su rika gaba da juna, musamman ma a yanzu da aka samu sasanci tsakanin Adam A Zango da Ali Nuhu bayan wata hatsaniya da ta afku a baya.”

Wani mai sharhi kan harkokin fina-finai a Kannywood, Aliyu Dalhatu wanda aka fi sani da Garkuwa, ya ce ya san halin ’yan fim sarai wajen daukar abu da zafi, don haka ya yi hasashe idan ’yan fim ba su bi abin a hankali ba za a samu sa-in-sa mai zafi a Kannywood sakamakon goyon bayan Atiku da Buhari.

“Na san halin ’ya fim tun ba yau ba, akwai su da daukar dumi a duk wani abu da suke yi, don haka idan ba a yi a hankali ba za a samu takaddama mai zafi a Kannywood, domin kowa zai so ya nuna ya isa, musamman ma da wadansu ’yan fim suka nuna fushinsu kan yadda aka gana da Buhari ba tare da su ba, da yawansu sun rika guna-guni,” Inji Dalhatu.

Ya ce abu ne mai kyau da ’yan fim suka yi na samun wadansu suna goyon bayan Buhari, wadansu kuma suna goyon bayan Atiku, domin bai kamata su jefa kwayayensu a kwando daya kamar yadda ’yan kabilar Ibo suka yi a zaben shekarar 2015 ba.

Ya ce, “A yanzu duk wanda ya lashe zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari, to zai yi da ’yan fim, domin dukkansu sun san suna da masoya a Kannywood, don haka ina so su hada kansu don su nemo wa Kannywood abubuwan da kowannensu zai amfana ba tare da bambancin ra’ayin a siyasa ba.