✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Adamawa: Kotun Koli za ta yanke hukunci kan karar Binani

Lauya ya jaddada wa alkalan Kotun Koli halascin nasarar Aisha Binani kamar yadda Hudu Ari ya sanar a lokacin da ake ci gaba da tattara…

Kotun Koli ta saurari karar da Jam’iyyar APC da ’yar takararta a zaben gwamnan Adamawa, Sanata Aishatu Dahiru Binani suke kalubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP.

Kotun za ta yanke hukunci ne bayan lauyan Binani ya jaddada wa alkalai halascin nasararta da aka sanar a lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.

A yau Litinin ne kwamitin alkalai mai mutane biyar karkashin jagorancin Mai Sahri’a John Inyang Okoro ya dage ci gaba da sauraron karar bayan sauraron jawaban lauyoyin bangarorin biyu.

Nan gaba kotun za ta sanar da zamanta na karshe inda za ta sanar da hukuncinta a kan karar da Binani ta daukaka zuwa kotun kolin.

Aisha Binani neman a ayyana ta a matsayin zababbiyar gwamnan jihar saboda zaben Fintiri da PDP na cike kura-kurai da saba dokar zabe ta 2022.

Kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara da ke Abuja sun yi watsi da karar da Sanata Aisha Binani kan zaben na ranar 18 ga Maris da 15 ga Afrilu.

Lauyanta, Akin Olujimi (SAN) ya ja hankalin kotun cewa bayyana sakamakon zaben da Kwamishinan Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (REC), Hudu Ari ta yi, da ke nuna cewa Binani ce ta yi nasara halastacce ne.

Hudu Ari ya bayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben a da ake tsaka da tattara sakamakon zaben, wanda hakan ya jawo ka-ce-na-ce.

Daga bisani hukumar ta soke sanarwar ta ba da umarni ci gaba da tattara sakamkon zaben wanda a karshe aka sanar cewa Gwamna Fintiri ya yi tazarce domin fara wa’adin mulkinsa na biyu.

A halin da ake ciki dai Hudu Ari na fuskantar shari’a kan riga-malam-masallacinsa wajen sanar da sakamakon zaben mai cike da rudani.