✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kananan Hukumomin Neja: APC ta lashe 22, PDP 1

Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin Kananan Hukumomi 22 cikin 25 na jihar Neja, wanda aka yi ranar Asabar. Yayin da  Jam’iyyar adawa ta PDP…

Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin Kananan Hukumomi 22 cikin 25 na jihar Neja, wanda aka yi ranar Asabar. Yayin da  Jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe Karamar Hukumar Gbako, kadai.

A cikin Kananan Hukumomin da APC ta lashe sun hada da: Bida, Agaie, Katcha, Lapai, Lavun, Kontagora, Rafi, Magama, Shiroro da Munya.

Sauran su ne: Suleja, Borgu, Gurara, Mariga, Mokwa, Paikoro, Wushishi, Chanchaga, Agwara, Edati, Rijau da kuma Bosso.

Shugaban Hukumar zabe na jihar (NSIEC) Alhaji Aminu Baba, ya ce a yanzu haka ana jiran sakamakon zaben Kananan Hukumomin Mashegu da Tafa.