Search
Subscribe
Zaben Kogi: An gano ma’aikatan zabe 30 da suka bace

Zaben Kogi: An gano ma’aikatan zabe 30 da suka bace

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce, an gano ma’aikatan Hukumar 30 da aka sanar da bacewar su, a wasu rumfunan zabe na zaben Gwamnan jihar Kogi da aka yi jiya Asabar.

Rotimi Lawrence Oyekanmi, Sakataren watsa labarai na Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu.

Rotimi Lawrence, ya ce a yanzu ma’aikatan suna cikin koshin lafiya ba tare da wani rauni ba, kuma sun isa gidajensu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin