✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Mai Mala Buni a Yobe alheri ne – Dauda Gombe

Babban Daraktan yaqin zaben xan takarar Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, na gida zuwa gida, Kwamared Dauda Muhammad Gombe, ya…

Babban Daraktan yaqin zaben xan takarar Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, na gida zuwa gida, Kwamared Dauda Muhammad Gombe, ya ce zaben xan takararsu ya zama Gwamna a Yobe alheri ne ga jihar, domin buxaxxiyar gwamnati ce da kowa zai shaida.

Kwamared Dauda Muhammad Gombe ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce idan al’ummar Jihar Yobe suka bai wa Mai Mala Buni quri’unsu a zaben da ke tafe ba za su yi kuka da shi ba, domin yadda Gwamna Gaidam ya yi  musu aiki shi ma haka zai yi har ma ya xora.

Ya ce bayan ya ci zabe zai bai wa bangaren lafiya da na ilimi muhimmanci sosai, sannan zai samar da ruwan sha da qarfafa wa mata da matasa, domin duk matsalar jihar ya san yadda zai magance ta.

“Kamar mata da suke ganin ana barinsu a baya, gwamnatin Mai Mala Buni za ta dama da su domin idan aka kafa gwamnati za a ba su kaso mai tsoka. Sannan iyaye mata da suke cikin gida ba za a bar su a baya ba wajen samar musu  da qananan sana’o’i da za su dogara da su,” inji shi.

A cewarsa APC ta xauko Mai Mala Buni ne ganin matashi ne xan zamani mai harka da kafafen sadarwa na zamani wanda ko ta nan al’umma suke ba shi shawari zai xauka, don ba mutum ne mai girman kai ba.

Kwamared Dauda Gombe, ya ce a bangaren tsaro, zai yi dukan mai yiwuwa wajen ganin ya sake daidaita sha’anin tsaron ya kuma bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu.