✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Ondo: INEC ta raba muhimman kaya

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta raba muhimman kayan zabe  gabanin zaben Gwamnan Jihar Ondo na ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020. Muhimman kayan da…

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta raba muhimman kayan zabe  gabanin zaben Gwamnan Jihar Ondo na ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020.

Muhimman kayan da INEC ta raba a ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Akure sun hada da takardun jefa kuri’a da na rubuta sakamakon zabe.

Tun ranar Litinin da aka kai kayan daga hedikwatar INEC, Abuja aka ajiye su a bankin a shirye-shiryen zaben na ranar Asabar.

Kwamishinan hukumar mai kula da jihohin Ondo, Edo da Legas, Adekunle Ogunmola da Kwamishinan Zabe na jihar Ondo, Rufus Akeju, ne suka lura da yadda aka gudanar da rabon kayan ga ofisoshin hukumar na kananan hukumomin jihar.

Wakilan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da jami’an tsaro da masu sa ido na daga cikin wadanda suka hallara domin ganin yadda aka gudanar da rabon kayan.