✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben raba raba-gardama: PDP ta bukaci a soke zaben Gwamnan Kano

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a gaggauta soke zaben takarar gwamnan da ake yi  yau  Asabar a jihar. Mukaddashin shugaban jam`iyyar PDP na Kano…

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a gaggauta soke zaben takarar gwamnan da ake yi  yau  Asabar a jihar.

Mukaddashin shugaban jam`iyyar PDP na Kano Alhaji Rabiu Suleiman Bichi, ya sanar da hakan ya ce, wannan zaben da ake yi a Kano na bogi kawai kuma wannan abin kunya ne a jihar Kano.

Alhaji Rabiu  ya ce, jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta ibi `yan daban siyasa da su zagaye duk rumfunan zabe 208 na jihar.