✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman lafiya: Gwamnan Zamfara ya halarci bikin Sharo

A ranar Talatar da ta gabata ce daruruwan mutane suka taru a harabar Kasuwar Duniya ta Gusau a Jihar Zamfara domin bikin sharo na Fulani,…

A ranar Talatar da ta gabata ce daruruwan mutane suka taru a harabar Kasuwar Duniya ta Gusau a Jihar Zamfara domin bikin sharo na Fulani, wanda Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sake dawo da shi domin nuna wa duniya cewa an samu zaman lafiya a jihar.

Gwamnan wanda shi ma ya halarci taron tare da Mataimakinsa, Barista Mahdi Aliyu Gusau, ya ce an sake dawo da bikin  sharo ne a cikin shirye-shiryen dawo da zaman lafiya a Jihar Zamfara, domin sun gano cewa barin Fulani su gudanar da taronsu ba tsangwama zai taimaka sosai wajen samar da aminci da yarda da juna a tsakanin jama’a.

Gwamna Matawalle da Mataimakinsa Mahdi, sun isa farfajiyar ce sanye da suturar Fulani rike da sanda, kuma bikin ya kayatar sosai kuma ya samu halartar manyan masu rike da mukamai a matakai daban-daban na gwamnati.

Makada da dama ne suka halarci bikin, inda suka nishadantar da mahalarta bikin da kada-kade da raye-raye. Sannan Fulanin sun nuna jin dadinsu bisa dawo da bikin nasu da suke matukar sha’awa sannan suka nuna cewa wannan yunkurin na Gwamna zai taimaka sosai wajen samar da zaman lafiya a tsakanin kabilun jihar.

Tun farko, Gwamna Matawalle ya ce shirye-shiryen gwamnatinsa na samar da dawwamammen zaman lafiya ya sanya Fulanin jihar sun samu kwanciyar hankali da natsuwar cewa lallai da gaske suke yi wajen sulhunta tsakanin al’umma.

“Wannan bikin na Sharo an sake dawo da shi ne domin a taru a taya juna murna, sannan a nuna wa duniya cewa an yafe wa juna abin da ya gabata domin samun kwanciyar hankali da lumana a Jihar Zamfara baki daya. Sannan ina da yakinin cewa shirinmu yana haifar da da mai ido domin duk dan Jihar Zamfara zai bayar da shaidar hakan,” inji shi.