✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamantakewar aure: Muhimman bayanai ga ma’aurata

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa Muhammad (SAW). Kamar yadda aka sani aure wani yanayi…

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa Muhammad (SAW). Kamar yadda aka sani aure wani yanayi ne da kan halatta zaman mace da namiji a matsayin ma’aurata domin samun dauwamar dan Adam a doron duniya ta hanya tsarkakakkiyar hanya. Aure hanya ce ta samun zaman jin dadi, kwanciyar hankali da walwala ga miji da mata, Manzon Allah (SAW) ya ce, “mafificinku shi ne wanda yake kyautata wa iyalinsa,” sannan a wani wurin ya ce “mafificiyar rayuwa samun mata ta kwarai” da wadannan zantuttuka zan yi wa bayanina tsani. A zamantakewar aure miji da mata suna da hakkoki da kowannensu ya kamata ya kiyaye.
Abu na farko da ya kamata ma’aurata su sani shi ne: Allah ne Ya halicce su daga rai guda, wato annabi Adamu, sannan Ya halicci matarsa Hauwa’u daga gare shi domin samun natsuwa, to hakkin Allah a nan shi ne su bauta maSa Shi kadai ba tare da gwamutsa wani abu ba wajen bautar. Wannan ya hada da dukkan sauran abubuwan da imani da Allah ya kunsa.
Bayan wannan ya kamata ma’aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora wa kowannensu.
Zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na mutu-ka-raba, domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga, sanin hakkokin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure. Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci kayyadadde ba, wato da an chinye kayan gara an gama zakin amarci a kama masifa a rabu ba, a’a tsari ne da Allah Ya shirya mana shi, sannan Ya tsara mana yadda zamantakewar za ta kasance. Ya dora ma kowannensu; miji da mata wadansu dokoki.  Idan muka ji tsoron Allah a cikin zaman auratayyarmu za mu kasance cikin wadancan biyun da na ambata a baya.
Ya kasance zaman aure ne wanda a kowane hali kuka sami kanku za ku iya jurewa cikin yanayin jin dadi ko akasin hakan; cikin halin lafiya  ko rashinta, domin a halin da muke ciki a yau za ka tarar daga karamin an abu yafaru tsakanin miji da mata, wani abin ma bai kamata ko wanda ke bakin kofar dakinku ya sani ba, amma haka za ka ga ana ta yamadidi da maganar har sai ta kai ga rabuwar wannan aure. Idan har za ku iya jure wa wahalhalun da kuka yi ta sha lokacin da kuke samartaka me zai hana ku karfafi aurenku ya zama na har abada ba?
A ’yan watanni a farkon aure har zuwa shekara daya ko biyu Allah Kan jarabci ma’aurata, amma duk wadannan abubuwa ba za su zama wani dalili ne na samun sabani a tsakaninku ba idan har kun san dalilin da ya sa kuke zaune a matsayin ma’aurata.
Yana da kyau ma’aurata su san halayyar junansu ta hanyar da babu yaudara, karya, ko cuwa-cuwa. Ya kasance ma’aurata sun fahimci hanyar da za su iya sulhunta kansu ba tare da wani mutum na uku ya shigo tsakaninsu ba, hakan na samuwa ne ta irin yadda kowannensu ya fahimci matsayinsa a zamansu na ma’aurata. Miji ya sani cewa ragamar tafiyar da gida a hannunsa take, a same shi mai kyautata wa  matarsa, wannan ya hada da mazauni, tufafi, ciyarwa da uwa uba koya mata addini. Haka ita mace ta sani hakkinta ne kula da mijinta ta wajen kare masa kanta da dukiyarsi da yi masa biyayya gwargwadon abin da bai saba wa shari’a ba.
Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tallafa wa juna a cikin halin zamantakewar gida, wato miji ya tallafa wa matarsa a wajen girki, shara, wanke-wanke da sauransu, ita kuma ta taimaka masa ta wajen wanki, guga da sauransu domin yin hakan na kara karfafa dankon zaman aure.
Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tausasa wa junansu. A matsayinka na maigida ka da ka kasance kullum mai ganin laifin matarka, kada kuma ka zamo mai yawan miti ga abin da aka yi maka na laifi. Hausawa na cewa ka gani, kaki gani, ka ji ka kuma ki ji, wannan na nufin ba kowane abu za ka gani ka yi magana ba, sai abin da ka ga ya wuce gona da iri, a tsawata a kan abin da ya dace kuma idan aka yi maka laifi ka yi magana aka ba ka hakuri, to ka hakura, kada ka zama mai riko.
A matsayinki na mata, ki kasance mai hakuri a kan duk abin da mijinki zai yi miki ko da kuwa a kan laifin da kike da gaskiya ne, domin maza a mafiya yawan lokuta ba sa son karbar laifi, to ki yi hakuri a irin wannan lokacin idan abin ya yi tsanani ma ki ba da hakuri, idan hakan ne zai zama mafita ko maslaha, don matar na tuba ba ta rasa miji.
Idan rai ya baci a rika kai zuciya nesa, a rika duba abin da yake ginshiki wanzuwar auren. Da fatan Allah Ya yi mana jagora; Ya ba mu ikon kiyaye zamantakewar auratayyarmu, amin.
Abdurrahman Abumaryam
07066741919 ko 08094727702
[email protected]
DUNIYAR MA’AURATA
Don maigida: Dabarun zama da  mata
Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Yau kuma ga bayani kan dabaru, hikimomi da sirrin da ya kamata magidanci ya yi amfani da su don ganin ya zauna lafiya da matansa kuma ya wanzar da cikakken adalci a tsakaninsu:
Assalamu Alaikum,
Na karanta dukkan bayananki a kan ladubban karin aure kuma na gamsu. Don Allah ki yi mana karin bayani a kan dabaru ko wasu hikimomin zama da mata sama da daya, domin zama da mace daya gami da yin adalci gare ta ba karamin abu ba ne, to ina kuma ga an tara har 4, kuma kowacce halinta daban, bukatunta daban; ya maigida zai bi don ya kasance ya zauna da kowaccensu lafiya kuma ya ba kowacce cikakken hakkinta na rayuwar aure?
-Baban Muhd, Kaduna
Dubara ta 1:Bin umarnin Allah Madaukaki
Babban abin da zai taimaki magidanci ya zauna da matarsa ko matansa lafiya shi ne, bin umarnin Allah Madaukakin Sarki kan yadda ya kamata ya yi zamantakewa da matansa. Alkur’ani ya kasance dauke da kyawawan bayanai ga magidanta kan yadda za su yi hulda da matansu. Za mu kawo wasu daga ciki hade da yin bayani kan yadda za a aiwatar da su don cin ribar rayuwar aure duniya da lahira.
1.    Alheri da kyautatawa: Allah SWT Ya yi umarni mai karfi ga magidanta cikin suratul Nisa’i Aya ta 19 cewa:
“….Kuma ku yi zamantakewa da su (mata) da alheri…”
Sannan idan muka dubi ayoyin cikin Suratul Bakara da suka yi bayani kan saki da sauran hanyoyin rabuwar aure (228-241), kusan kowace aya sai an yi umarni da aikata alheri da kyautatawa ga mata a cikinta; to a maganar saki ma ke nan, ina ga shi zaman auren kuma?
Don haka sai magidanci ya daure ya huldanci dukkan matansa da alheri da kyautatawa, ya sa wannan niyya a zuciyarsa, ya tabbatar da ita kuma ya karfafa ta; ya kasance a kowane lokaci; na dadi ko na rashinsa; na wahala ko na kwanciyar hankali, alheri da kyautatawa su ne za su yi wa maigida jagoranci wajen hulda da matansa; indai maigida ya rike wannan kuma ya dage da aikata shi, to da wuya ya samu matsala cikin rayuwar aure da matansa, dama abin da ke kawo matsala ga rayuwar dan Adam shi ne, kin bin umarnin Allah Madaukakin Sarki da bin son zuciya da zugar shaidan.
2.    Su tufa ne gare ku
Allah Madaukaki ya bayyana ga magidanta a cikin aya ta 187 cikin Suratul Bakara cewa: “Lallai ku tufa ne gare su, su ma tufa ne gare ku.”
To ya mutum yake wa tufarsa in har yana son ta yi masa amfanin da ya kamata; Watau ta suturta shi, ta kawata shi, ta ba shi kariya daga sanyi ko kura ko ta fito da kimarsa ko ta daga darajarsa? Ai dole sai ya kula da ita sosai, daga ta yi dauda ya wanke ta ya goge, ya feshe ta da turare, sannan ya ajiye ta a wuri mai kyau inda kura ko wani datti ba za su iske ta ba ballanta su bata ta; to haka ya kamata a ce maigida ya aikata ga matansa; ya kula da su ta hanyar samar da duk wani abubuwan bukatar rayuwa gare su; ya karrama su ta hanyar kyautatawa gare su da yin kyakkyawar zamantakewa da su; ya tattala su ta hanyar ba su kariya daga duk wani abu da ka iya cutar da su a rayuwarsu ta duniya da lahira.
Kuma ya aikata haka ga duk matan da yake aure ba wai ya zabi wata ko wasu ya kyale sauran ba, domin in tufa daya mutum yake tattalawa da adanawa, to ita kadai za ta yi masa amfanin da ya kamata lokacin da ya sanya ta, amma sauran da ya bari da dauda ko wata yagar da ba dinke ba, ko a yamutse ba guga, duk lokacin da ya sanya su ba za su yi amfani gare shi ba, sai dai su rage masa kima da daraja ko su munanta masa kamanni. Kowace irin tufa ana sanyata ne da irin yanayinta ko siffarta, to haka ko wace mace sai a zauna da ita da irin yanayinta ko halayyarta, don samun sauki da dadin rayuwar aure.
3.    Matanku gonakinku ne…
Haka kuma a cikin aya ta 223 cikin Suratul Bakara dai, Allah Ya ce:
“Matanku gonakinku ne, (don haka) ku je ga gonakinku ta inda ranku ya yi muku, kuma ku gabatar da alheri domin kawunanku.”
To yaya manomi ya kamata ya yi wa gonarsa idan har yana son ta ba da amfani mai kyau? Sai ya kula da ita sosai ta kowane fannin da take bukatar kulawa; ta hanyar nome ta da yin kaibe; sa mata takin da ya dace da ita; wata sa’in ma har da tsaronta don kare ta daga dabbobi da ka iya shiga su yi barna a cikinta.
Kuma a ce manomin da ke da gona hudu, ai in yana son dukkansu su yi masa amfani; su ba da yabanya mai kyau, ai dole sai ya kula da su ta hanyar da ta dace- kasar wata gonar ta fi bukatar taki don ta ba da amfani mai kyau, wata gonar kuma ita ta fi bukatar isasshen ruwa sama da takin, wata kuma yawan kaibe take so sama da komai, to kowacce sai a yi mata abin da ta fi bukata don a samu amfani mai yawa daga gare ta. Kowace gona yakan kasance akwai inda manomi kan samu matsala da ita, amma saboda alheran da za ta kawo masa sai ya yi ta hakuri haka nan ya yi ta noma abinsa; to kamar haka magidanci ya kamata ya huldanci matansa; kamar yadda Madaukakin Sarki Yake cewa:
“Sa’annan idan kun ki su, akwai tsammanin ku ki wani abu alhali Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa.” Nisaa’i, 19.
Don haka sai a yi ta hakuri da raunin mata da karkacewarsu don fatan samun irin wannan alheri da Allah Madaukakin Sarki Ya ambata.