✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan iya shafe Afghanistan daga doron kasa cikin mako – Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya fadi a farkon makon nan cewa, zai iya kawo karshen yakin da Amurka ke yi a kasar Afghanistan cikin…

Shugaba Donald Trump na Amurka ya fadi a farkon makon nan cewa, zai iya kawo karshen yakin da Amurka ke yi a kasar Afghanistan cikin sauki, ta hanyar ruguza dukkan kasar, sai dai kawai ba ya son salwantar rayukan mutum miliyan 10, da hakan zai janyo.

“Aikinmu ya yi kama ne da na ’yan sanda. Ba yaki muke yi ba. Idan dai muna son mu yi yaki a kasar; kuma a yi galaba, to zan iya yin galabar, cikin mako guda kawai,” kamar  yadda Shugaba Trump ya fada wa manema labarai, yayin da yake ganawa da Firayi Minsitan Pakistan, Imran Khan a ofishinsa na Obal da ke Fadar White House, inda ya kara da cewa “Ba na son in salwantar da rayuka miliyan 10 ne,” inji Trump.

Al’ummar kasar Afghanistan dai sun kai kimanin mutum miliyan 35.

“Ina da tsare-tsare a kan Afghanistan, da in har ina son in yi galaba a yakin; to ko shakka babu, za a shafe kasar dungurungum daga doron kasa; za ta zama tarihi cikin kwana 10 kacal,” inji Trump.

A daukacin ganawar tasa da manema labarai, Shugaba Trump, ya yi ta babatu ne game da dadadden yaki a cikin tarihi da Amurkar ta shiga yi, a Afghanistan din.

“Idan dai har muna son galabar, to tabbas za mu yi….. Ina da tsarin da in aka bi shi, to kuwa za mu yi galaba cikin kankanen lokaci,” inji Trump. Ya ci gaba da cewa: “Muna kasar ce kawai; amma ba yaki muke yi ba. ’Mutanen Afghanistan, na gina gidajen mai da na iskar gas. Suna kuma sake gina makarantu da kansu. Amma mu Amurkawa, ba aikinmu ba ne; aikinsu ne su yi haka.”

Ba a dai san cewa ko an gabatar wa Mista Trump din, tsare-tsaren matakan sojin da za su iya kaiwa ga salwantar da rayukan fararen hular Afghanistan din ko kuwa a’a ba. Sai dai wani tsohon hafsan soja, Janar Barry McCaffrey (mai ritaya), ya nuna kaduwarsa game da kalaman na Trump.

Sakamakon nuna damuwarsa game da babatun da Trump din ya yi ta yi da manema labarai a kan yakin Afghanistan din, shi ma Firayi Ministan Pakistan ya furta cewa kasarsa ta yi nazari kuma ta zartar da yin amfani da makamin nukiliya a kan kasar Afghanistan din, inda za su kashe miliyoyin ’yan kasar a matsayin hanyar kawo karshen wannan yakin.

Shugaba Trump ya tuna yadda Amurka ta jefa wani bam dinta mai karfin gaske a kan kasar Afghanistan a shekarar 2017, ya kuma ce Ma’aikatar Tsaron kasar wato Pentagon tana tunanin sake amfani da ire-iren wadannan bama-bamai a Afghanistan. “Sun gaya mini cewa, za su ci gaba da kera makamancin wannan bam, amma na hana su,” inji shi.

Muhimmin cikin ajendodin da Trump ya gabatar wa takwaransa na Pakistan, Imran Khan, shi ne bukatar Pakistan din ta taimaka wajen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin gwamnatin Afghanistan da Kungiyar Taliban; don Amurka ta gaggauta janye dakarunta daga kasar dungurumgum.