✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi kokarin samar wa matasa ayyukan yi – Jarman Wunti

Mai neman tsayawa takarar Shugaban Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Sale Abubakar Sale, Jarman Wunti ya ce idan…

Mai neman tsayawa takarar Shugaban Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Sale Abubakar Sale, Jarman Wunti ya ce idan ya samu nasara, zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya samar wa dubban matasan karamar hukumar ayyukan yi. Alhaji Sale Abubakar Sale ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya., inda ya ce kowa ya san babbar matsalar da take damun al’ummar Karamar Hukumar Toro, ita ce ta rashin ayyukan yi ga matasa.

Ya ce akwai matasa da suka kammala manyan  makarantu sama da  170  da ba su da ayyukan yi a karamar hukumar. Haka kuma akwai ’yan makaranta da dama da suke son su ci gaba da karatu da kuma matasan da suke sana’a, amma da ba su da jari.

“Za mu yi iyakar kokarinmu wajen ganin wadannan matasa sun samu abubuwan da za su yi musamman a bangaren noma, domin muna da  kasar  noma mai albarka  a wannan karamar hukuma. Kuma  mun shahara wajen  noman dawa da masara da waken soya. A duk Najeriya an san sunan wannan karamar hukuma wajen noman dankalin Hausa. Don haka za mu inganta wannan noma, ta yadda matasanmu za su samu abin da za su dogara da kansu,” inji shi.

Ya ce a bangaren ma’adanai a duk Jihar Bauchi babu inda ya kai Karamar Hukumar Toro yawan ma’adanai, domin akwai man fetur da gwal da kuza da za a yi amfani da su wajen inganta rayuwar al’ummar karamar hukuma da Najeriya baki daya. Don haka ya ba da tabbacin cewa idan ya samu nasara, zai tsaya wajen ganin al’ummarsa sun ci gajiyar wannan arziki da Allah Ya ba su.

Ya yi kira ga kananan hukumomin Najeriya su daina dogara da kudaden da ake turo masu daga asusun tarayya, saboda wadannan kudade ba za su isa su rika yi wa al’ummominsu ayyukan ci gaba ba. Don haka ya zama wajibi shugabannin kananan hukumomin, su tashi su nemo wasu hanyoyin da za su rika samun kudaden shiga domin su rika yi wa al’ummominsu ayyukan ci gaban kasa.