Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zanga-zanga ta zama rikici a Sudan

Shugaban Sudan Omar al-Bashar

An ji karar harbe-harben bindiga a wajen hedkwatar Rundunar Sojin Sudan da ke birnin Khartoum inda a nan ne dubban mutanen kasar ke zanga-zangar zaman dirshan.

Mutanen kasar suna zanga-zanga ce suna neman Shugaban Kasar Omar al-Bashir ya sauka daga kan karagar mulki.

ADVERTISEMENT

Wadanda suka ga lamarin sun ce sun ga mutane suna gudu domin neman mafaka a lokacin da aka fara harbin.

Harbe-harben sun yi kama da kokarin gwamnati na karshe domin tarwatsa zanga-zangar.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Ahmed Mahmoud ya shaida wa BBC cewa jami’an tsaro na sirri “Sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashi,” domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Ya ce sojoji dauke da makamai sun killace masu zanga-zanga cikin gidajensu.

Ya ce, “Babu amfani ga Omar al-Bashir ya ci gaba da amfani da ’yan barandansa domin hana mu zanga-zanga kan hanyoyi kuma ba za mu je ko ina ba.’’

Akalla sojoji biyu ne aka bayar da rahoton mutuwarsu tun da aka fara gudanar da zanga-zangar a wajen hedkwatar rundunar sojojin.

Kokarin da jami’an tsaro na sirri suka yi a baya domin tarwatsa masu zanga-zangar ya jawo sojoji sun shiga domin kare masu zanga-zangar.

An ta samun kiraye-kiraye daga kasashe daban-daban ga gwamnatin Sudan kan ta guji amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Shugaba al-Bashir ya yi kira domin a zauna a tattaunawa kan yadda za a ga an samu zaman lafiya.

Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar a ranar Litinin ya bayyana cewa masu zanga-zangar 17 aka kashe sai kuma mutum 15 suka jikkata.

Ya ce jami’an tsaro 45 ne suka samu raunuka a kokarin da suke yi na tarwatsa masu zanga-zangar.

Ministan ya ce a halin yanzu kusan mutum 2500 ne aka kama.

Wannan zanga-zangar da ake yi ta ta nuna kin jini ga Shugaba Bashir an fara ta ce watannin da suka gabata.

Shugaba Bashir ya fara mulkin kasar tun 1989.

Asalin zanga-zangar ta fara ce lokacin da aka samu hauhawar farashin kayayyaki a kasuwa inda daga baya kuma zanga-zangar ta sauya akala masu yi suna bukatar Shugaban ya yi murabus.

Ana sukar mulkin Bashir da take hakkin dan Adam. Kuma Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ta bayar da takardar sammaci kama shi sakamakon zarge-zargen da ake yi masa na kisan kiyashi da kuma laifuffukan da suka shafi yaki da kuma laifin take hakkin dan Adam.

Amurka ta saka wa kasar takunkumi shekara 20 da suka gabata inda Amurkar ke zargin Khartoum da daukar nauyin kungiyoyin ’yan ta’adda kamar yadda BBC ya ruwaito.

A bara, darajar kudin Sudan ya fadi warwas wanda hakan ya yi sanadiyar samun tashin gwauron zabo kan farashin kayayyaki.