✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga: ‘Yan PDP na neman a kori Maibasira

‘Yan Jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga neman uwar jam’iyyar ta sallami Sakataren Kudinta na Kasa Abdullahi Maibasira. Zanga-zangar na zargin Maibasira da hada baki da…

‘Yan Jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga neman uwar jam’iyyar ta sallami Sakataren Kudinta na Kasa Abdullahi Maibasira.

Zanga-zangar na zargin Maibasira da hada baki da gwamnatin Jam’iyyar APC a Jihar Neja wajen yi wa PDP zagon kasa.

Boren a zauren taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa a Ofishin Jam’iyyar na Legas House a Abuja, na zuwa ne washegarin ranar da wasu ‘yan jam’iyyar daga Jihar ta Neja suka yi zanga-zanga a hedikwatar uwar jam’iyyar kan zaben shugabanninta na Kananan hukumomi.

Masu zanga-zangar ranar Talata sun zargi kwamitin da uwar jam’iyyar ta tura domin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da ba da damar yin murdiya a zaben.

Karin bayani na tafe…