✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaratan ’yan kwallon Najeriya da suke wakiltar wasu kasashe

Idan ana maganar fitar da zaratan matasan ’yan kwallon kafa a duniya, Najeriya ba kanwar lasa ba ce, domin idan ba ta zo ta daya…

Idan ana maganar fitar da zaratan matasan ’yan kwallon kafa a duniya, Najeriya ba kanwar lasa ba ce, domin idan ba ta zo ta daya ba za ta kasance a cikin ukun farko.

Sai dai akwai damuwa kan yadda ’yan wasan kwallon na Najeriya ke karkon kifi, inda ba su cika dadewa suna haskakawa ba.

A lokuta da dama sukan fito da karfinsu, amma cikin kankanen lokaci sai a neme su a rasa.

Daga cikin ’yan wasan da suka dan dade ana jin duriyarsu, akwai Mikel Obi duk da cewa shi ma yakan yi kwan-gaba-kwan-baya, sai Obafemi Martins da Kanu da wadansu kalilan.

A yanzu Kungiyar Super Eagles tana Najeriya tana da zaratan matasan ’yan kwallo, irin su Samuel Chukwueze da Simon Moses da John Aribo da Bictor Oshimhen da sauransu, amma kasar ta yi rashin wadansu fitattun ’yan wasan da duniya ke ji da su.

Abin takaicin shi ne, yadda wadansu ’yan asalin Najeriya ke wakiltar wasu kasashen duniya, kuma tauraronsu ke haskakawa a duniyar kwallon kafa.

Hakan ya sa Aminiya ta rairayo wadansu zaratan ’yan wasa da tauraronsu ke haskakawa a duniyar kwallon kafa a yanzu, wadanda kuma asalinsu ’yan Najeriya ne.

Ross Barkley: Ingila da Chelsea

Dan wasan tsakiyar Kungiyar Chelsea, Ross Barkley mahaifinsa mai suna Peter Effanga dan Najeriya ne. Yanzu haka yana wakiltar Chelsea ce, kuma duk mai kallon gasar Firimiya ta Ingila zai yi wuya bai san sunansa ba.

Dabid Alaba: Austeriya da Bayern Munich

Dan wasan bayan Bayern Munich, Dabid Alaba yana daya daga cikin taurarin ’yan wasa da zamani ke yi da su. Mahaifinsa dan Najeriya ne, kuma ana kiransa da sunan Olatokunbo da Yarbanci. A kakar 2012/2013 da Bayern Munich ta lashe gasar Kofin Zakarun Turai, an nuno Alaba rike da tutar Najeriya da ta kasar Austeriya da yake wakilta. Sannan ya taba bayyana cewa ya so ya wakilci Najeriya a gasar ’yan kasa da shekara 17.

Dele Alli: Tottenham da Ingila

Asalin suna mahaifinsa Bamidele, wanda sunan Yarbawa ne, amma mahaifiyarsa ’yar Ingila ce. A shekarar 2015, wani tsohon dan wasan Ingila wanda shi ma asalinsa dan Najeriya ne, John Fashanu ya so ya jawo hankalin Dele Ali da ya zo ya buga wa Najeriya, amma abin ya ci tura.

Tammy Abraham: Chelsea da Ingila

Asalin sunansa Kebin Oghenetega Tamaraebi Bakumo-Abraham, kuma a kwanakin nan ma an yi ta yin maganar yiwuwar kiransa ya buga wa Najeriya, amma ya ci tura, duk da kasancewar mahaifinsa, wanda dan Najeriya aboki ne ga Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF). Bayan tata-burza da aka yi, daga baya sai ya zabi ya wakilci Ingila.

Jordon Ibe:  Bournemouth da Ingila

Asalin sunansa Jordon Ashley Femi Ibe, kuma mahaifinsa dan Najeriya ne. Yanzu haka yana cikin zaratan ’yan wasan kungiyar Bournemouth. A shekarar 2015, kocin Najeriya Sunday Oliseh ya yi kokarin jawo hankalinsa ya buga wa Najeriya, amma abin ya ci tura.

Fikayo Tomori: Chelsea da Ingila

Asalin sunansa Oluwafikayomi Oluwadamilola “Fikayo” Tomori, kuma iyayensa ’yan Najeriya ne, aka haife shi a Kanada, sannan ya girma a Ingila. Ya wakilci kasar Kanada a wasannin kasa da shekara 17 da 20, amma daga bisani ya zabi ya koma Ingila da taka leda, duk da cewa Najeriya ta yi kokarin daukansa.

Stefano Chuka Okaka: Italiya da Udinese

Dan wasan gaban Udinese Stefano Chuka Okaka, iyayensa baki daya ’yan Najeriya ne, amma ya samu tikitin zama dan kasar Italiya a shekarar 2007. Sannan a shekarar 2009 ya wakilci kasar a gasar ’yan kasa da shekara 19. Yanzu haka yana taka leda ce da kungiyar Udinese na rukunin Seria A na Italiya.

Sidney Sam: Jamus da SCR Altach

Tsohon dan wasan Bayern Liberkusen, wanda ya yi fice a taka leda a tsakiya, shi ma mahaifinsa dan Najeriya ne, amma bai taba buga wa Najeriya ba. A lokacin da Samson Siasia ke kocin Najeriya, ya yi kokarin dauko Sam ya buga wa Najeriya, abin ya ci tura, inda ya ce ya kira shi sama da sau 10, sannan ya tura masa sakon waya, amma bai amsa ba.

Akwai wadansu da dama da suke buga wa wasu kasashen da ba su yi fice ba, kamar su Emma Sarki da ya buga wa Najeriya a wasannin kasa da shekara 17 da 20 da 23, amma daga baya ya koma Haiti da Oguchi Onyenwu da yake buga wa Amurka da Nedum Onuoha da ke buga wa Ingila da sauransu.