Da Dumi Dumi

Zariya 2019: Taron Gizagawan Najeriya Domin Tunawa da Marigayi Mahmoon Baba-Ahmad

A gobe Asabar 17-04-1441 (Bayan Hijira), daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) idan Allah Ya kai mu, Gizagawan Najeriya za su hallara a babban zauren taro na Kwalejin Barewa da ke Zariya a Jihar Kaduna, domin gudanar da taronsu na bana. A bana taron zai samu halartar babban mai jawabi, Farfesa Ibrahim Malumfashi, na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda zai gabatar da mukala dangane da Gudunmawar Jaridun Hausa ga Al’umma. Haka kuma taron zai gudana ne, musamman domin tunawa da daya daga cikin iyayen kungiyar, marigayi Malam Mahmoon Baba-Ahmad. Marigayin, kafin rasuwarsa ya kasance shahararren dan jarida, kuma daya daga cikin marubuta a jaridar Aminiya. Don haka, domin tunawa da gudunmawar da Malam Mahmoon ya ba da wajen fadakarwa ga al’umma, GIZAGO (08065576011) ya zakulo daya daga cikin mukalolinsa da ya taba rubutawa a shafinsa na MATASHIYA a shekarun baya, mai taken “Magance Matsalar Noma A Arewa” ya kawo ta nan:

 

A wasu wurare a kuryar Arewacin kasar nan, damina na shirin yin ban-kwana da manoma kuma nan da mako uku ko hudu za ta kawo karshe a tsakiyar yankin Arewa, manoma za su dukufa girbin abin da suka yi ta wahalar nomawa a gonakinsu. Bisa ga dukkan alamu an samu damina mai albarka a bana kuma manoma sun dukufa noma dan abin da za su iya domin ciyar da iyali. Da yawansu kuma ba su noma albarkatun da za a sayar a kasuwanni don samun na zaman gari ba, ko kuma wadanda za a sarrafa a masana’antu don kara habaka tattalin arzikin kasa.

A Najeriya dai a Arewacin kasar nan ne ake noma, domin kuwa a nan ne ake da wadatacciya kuma yalwatacciyar kasar noma mai albarka a dukkan jihohi 19 na yankin, wadanda suke da albarka kuma babu abin da ba a iya nomawa a cikinsu. Amma abin takaici game da haka shi ne, manoman Arewa ba su iya cin gajiyar wadannan filayen noma masu dimbin albarka saboda rashin kayayyakin noma irin na zamani da kuma kayayyakin inganta aikin gona, kamar takin zamani iri-iri, kuma a wadace da magungunan feshi don kashe ciyawa da kwarin da ke yin illa ga amfani, walau kafin girbewa ko  bayan an kawar zuwa rumfuna da ma’adana. Baicin haka kuma manoma ba su iya samun tallafin gwamnati yadda ya kamata, kuma a kan kari. Hatta ’yan kudin da za su nemi agaji don habaka aikace-aikacensu ba su iya samu cikin kwanciyar hankali.

Dalilan da suke haddasa wadanan al’amura masu ban takaici a fili suke, ba sai an je nesa ba kafin a gano su. Da farko dai dukkan kamfanonin yin takin zamani da na maganin kwari da wuraren sarrafawa ko alkinta amfanin gona, duk a Kudancin kasar nan suke ba a Arewa ba, inda ake yin noman. ’Yan kasuwar Kudu ne ke shigo da kayayyakin noma na zamani da magungunan kashe kwari da ciyawa, har ma da takin zamani. Daga can Kudu ne ake kawo su yankin Arewa a sayar da dan karen tsada kuma ba a lokacin da ya dace ba, sai lokacin amfani da su ya yi kusan karewa. Yawancin bankunan da ke sarrafa kudaden da Gwamnatin Tarayya kan bayarwa ta hannun Babban Bankin Najeriya ba na ’yan Arewa ba ne, ko kuma a ce manajojinsu ba ’yan Arewa ba ne, saboda haka nan ba su damuwa idan har manoman Arewa ba su samu kudaden ba a kan kari, kamar yadda ake zarginsu game da haka.

ADVERTISEMENT

Muddin ana son habaka aikin gona yadda ya kamata a kasar nan sai an fara da inganta matsayin manoman Arewa da kuma yadda suke gudanar da sana’ar noma da kakkafa musu masana’antu ko kamfanonin da za su rika samar musu da dukkan abubuwan da suke bukata a-kai-a-kai, ba sai an kawo musu daga Kudancin kasar nan ba. Wajibi ne a samar da wurare ko ma’aikatun da za a  rika sarrafa dimbin albarkatun da ake nomawa a kasar nan, kamar samfarerar shinkafa da ta alkama kuma a samar da wuraren adana amfanin da manoma suka samar, domin rashin alkinta su ne ke karya gwiwoyin manoman da ke nomawa su kuma rasa yadda za su yi da su da kaka. Wajibi ne kuma a koya wa manoma dabaru da hanyoyin gyaggyara amfanin da suka samu da yadda za su ajiye su a rumbuna tare da taimakon magungunan kare su daga kwari.

Baicin haka kuma ya kamata a kafa wani kwamiti da zai binciki dalilan da suke hana manoman Arewa sakin jiki su noma auduga wadatacciya, don amfanin masakun kasar nan da kuma gyadar da za ta farfado da masana’antun mai a jihohin Kano da Kaduna da Katsina da kuma raken da zai dawo da martabar kamfanin yin sukari na Bachita da Numan. Yin haka zai taimaka wajen noma wadannan albarkatun, ya kuma kara karfafa matsayin masana’antun da za su wanzar da arzikin da zai amfani jama’ar kasa, ya kuma rage yawan dimbin marasa aikin yi.

Da gangan ne dai ake ta molon-ka game da farfado da aikin gona a Arewa tunda dai babu alamun magance wadannan matsaloli da aka zayyana, wadanda suke sanadiyyar kashe gwiwoyin manoman da ke noma cikin wahala, ba su kuma samun ribar da za ta hutasshe su daga wahalhalun da suka fuskanta a gonakinsu. Idan kuma har ana so manoman Arewa su ji dadi wajen noma yadda ya kamata, to sai a taimaka su kakkafa bankunan da za su taimaka da kudaden da suke bukata na kashin kansu, inda gwamnati za ta rika tuttura musu kudaden rance kai-tsaye ba tare da bi ta kan bankunan da ba su biya musu wata bukata ba game da haka.

A fadin Afirka kafatan, babu wata nahiya kamar ta Arewacin Najeriya mai dimbin albarkatu da ma’adinai da yawan bil-Adama, kuma wadannan sun isa a ce ita ce kan gaba wajen samar da abinci don ciyar da dimbin jama’ar cikinta da samar da dukkan albarkatun gonar da masana’antu ke bukata a nan cikin gida, a kuma fitar da ragowar zuwa wasu kasashe don sayarwa, daidai da manufar Gwamnatin Muhammadu Buhari.

Amma kash! Mutanen Arewa a halin yanzu ba su samun damar cin moriyar tallafin da gwamnati ke bayarwa, sai wadansu ne can da ba su aikin gona ke ci da guminsu, suna nika ne kawai wadansu kuma na kwashe garin. Ba ’yan Arewa damar cin moriyar aikin gona ne kadai zai sa yankin Arewacin kasar nan, inda nan ne ake noman, ya wadatu da masana’antu, manoman yankin su zame manyan attajirai da hamshakan ’yan kasuwar da za su yi dillancin dukkan kayayyakin noma da ake bukata da kuma na amfanin yankinsu, maimakon yadda a ’yan shekarun baya aka mayar da yankin Arewa kasuwar kayayyakin noma da kamfanonin ’yan Kudu suka samar ko suka shigo da su kasar nan daga kasashen ketare. Ba wani abu ba ne kuwa ya jawo haka illa sakacin da su ’yan Arewar da kansu suka yi da noma, a matsayinsa na almakashin yanke talauci, suka shiga hauma-hauma. Ya kamata ’yan Arewa su farka, su rungumi noma domin yanke wa kansu talauci da magance koma-bayan da yankinsu ke ciki.

 

Share