✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar su Daurawa ga Kwankwaso ta bar baya da kura a Kano

A kwanakin baya ne Kwamanda Janar na Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci wadansu malamai 100, suka kai ziyarar goyon…

A kwanakin baya ne Kwamanda Janar na Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci wadansu malamai 100, suka kai ziyarar goyon baya ga madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Sai dai kuma wannan ziyara ta bar baya da kura, inda a yanzu haka Kwmanda Janar din yake neman rasa kujerarsa.

Binciken da Aminiya ta gudanar a Hukumar Hisbah, ta gano cewa an rufe ofishin Kwamanda Janar din da sabon makulli, inda kuma aka canja wa Sakatarensa wurin aiki.

Majiyar Aminiya ta kara da cewa daukar matakin ya biyo bayan taro da shugabannin Hukumar Gudanarwar Hisba suka yi ne, inda suka yanke shawarar cewa a cire wancan makullin ofishin Kwamanda Janar din tare da sanya sabon makulli da niyyar tsare kayayyakin da suke cikin ofishin. “Kin san da yake an yi wata guda Kwamanda ba ya zuwa ofis, tun daga lokacin da ya je Umara kuma a yanzu da ya dawo bai zo ofis ba. Wannan ya sa aka yanke shawarar a sake wa ofishin nasa makulli don kara kulawa da kayayyakinsa da ke cikin ofishin. Kuma sakatarensa ya samu aikin yi, maimakon zama haka kawai da yake yi,” inji wata majiya.

Sai dai a tattaunwar da Aminiya ta yi da Sheikh Aminu Daurawa ta tarho, ya bayyana cewa ya samu wannan labari sai dai har zuwa yanzu babu wanda ya sanar da shi a hukumance game da wanann mataki da hukumar ta dauka.

“Da zan tafi Umara na bayar da aikin rikon kwarya ga Mataimakina. Kuma da za a yi wannan aiki na gyaran ofishina babu wanda a hukumance ya tuntube ni a kan hakan. Sai dai labari kawai na ji a gari kuma sakatarena yana aiki, idan na samu takarda zan sa ya je ya kai ta wurin da ya kamata ko kuma idan bukatar gaggawa ta taso in kira shi don gabatar da wasu muhimman ayyuka. Amma rana tsaka aka je aka fitar da shi ta karfin tsiya daga ofishin. Ni ban san abin da hakan ake nufi ba,” inji shi.

Tun farko Sheikh Daurwa ya yi wa Aminiya karin haske game da dalilin kai waccan ziyara ga Sanata Kwankwaso, inda ya ce sun je ne don a kwantar da wutar da ta tashi, wanda ba don sun shiga cikin maganar ba, to da Allah ne kadai Ya san irin rigimar da za ta barke a jihar, tsakanin malaman jihar da kuma ’yan kungiyar Kwankwasiyya.

“Akwai kalaman da Sanata Kwankwaso ya yi a kan wadansu malamai, inda ya janyo cece-kuce har wadansu malamai suka rika kiran Kwankwason da sunayen batanci, cewa ya yi ridda da sauransu. Haka malaman sun dauki niyyar cin mutuncin Kwankwaso a hudubobinsu na ranar Juma’ar da ta gabata. A bangaren magoya bayan Kwankwason kuma su ma sun sha alwashin mayar da maratani ga duk malamin da ya taba mutuncin shugabansu.

“To a matsayinmu na malamai a Jihar Kano sai muka ga ya dace mu shiga cikin lamarin, inda muka je muka ba Kwankwaso hakuri. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, domin magoya bayan Kwankwason ba su mayar da martani ba duk da cewa malaman sun zazzagi shugaban nasu a lokacin hudubobinsu,” inji shi.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa malamin da aka ji yana maganar siyasa a wajen ziyarar ba a cikin ayarinsu yake ba. “Dama shi wannan malami a wannan wuri muka same shi saboda haka ba ya cikin ayarinmu,” inji shi.

Ya ce, a iya saninsa har yanzu shi ne Kwamanda Janar na Hukumar Hisba har zuwa lokacin da za a ji wani bayani sabaninwannan daga Gwamnatin Jihar Kano. “Lokacin da za a dauke ni takarda aka rubuto mini kuma a yanzu babu wanda ya ba ni takardar cewa an cire ni. Don haka har yanzu ni ne Shugaban Hukumar Hisba, sai dai idan mun ji wani abu sabanin haka daga gwamnati,” inji shi.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Darakta Janar na Hukumar Hisba, Malam Abba Sa’id Sufi ya musanta batun canja makullin ofishin Kwamanda Janar din tare da musanta canja wa sakatarensa wurin aiki. “Babu gaskiya a cikin wannan magana. Ba a canja makullin ofishin Kwamandan ba, haka ba a canja wa sakatarensa wurin aiki ba. Wannan ba wani abu ba ne illa munafuncin masu munafunci da suka kitsa don kada a zauna lafiya,” inji shi.