Da Dumi Dumi

Zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari (6)

Saboda haka, daga karshen wannan tambihi abin da zan kokarta yi shi ne in kawo maka wadansu shawarwari da nake ganin in an yi aiki da su za su iya kawo sauki daga cikin wasu matse-matsen da ke damun al’ummar kasar nan, insha Allahu.

Ya sugabana Buhari, shawarar farko da zan iya ba ka a dan wannan tsakani ba ta wuce in ce ka natsu ka fahimci inda matsalar kasar nan take a zahiri ba. Eh, a can baya na kawo maka manyan-manyan shingayen da ke gabanka a tsawon mako 5 ke nan, amma daga abin da na amaye, ina jin ba babban shingen da yake gabanka, wanda kuma shi ne babban tarnakin hana gwamnatinka ci gaba irin talakan kasar nan. In na ce talaka ina magana kan al’ummar da kake mulka, kama daga ministocinka da gwamnoninka da ‘yan majalisarka da masu arzikin kasarka da sarakunan kasarka da ma’aikatan kasarka da malaman kasarka da daliban kasarka da ’yan siyasar kasarka, kai da duk wani da ke shakar iskar kasar nan, har da ni mai wannan rubutun.

Ka sani ya Shugaba Buhari mu ne ummul haba’isin matsalolin da kake ta fafutikar ka kawar ko ka samar da mafita ga kasar nan, idan kuma mu ba mun gyaru ba, ba wani abu da za ka iya yi domin kawo sauki a kasar, za ka gama rawarka da tsalle ne, ka komo gida Kaduna ko Daura, ba tare da ka tsinana komi ba, domin ni da sauran irina daga cikin talakawan kasar nan, mun san ba wani abu da za ka iya yi, irin abin nan ne na ‘ba ka ce kai mai gaskiya ba ne, mai rikon amana da hana cin hanci da rashawa ba ne, to je ka ma ga yadda za ka kawo gyara ga kasar nan!’

Na san ya zuwa yanzu ka fara tunanin wai ko dai na tabu ne, domin nan a baya na gama caccakarka da gwamnatinka, ina kuma tula laifin duk a kanka, yanzu kuma na yi wata doguwar zamiya da nufin dora laifin a kan kowa da kowa, ba kai kadai ba. Hakan na iya zama gaskiya, amma kada ka yi saurin yanke hukunci game da zancena, saurare ni ka ji inda zan diga aya tukuna.

Na zarge ka bisa ga kasa yin katabus ga dukkan matsalolin da na zayyano a Najeriya  a can baya da gangan ne, irin abin nan ne da Ingilawa ke cewa, duk tsuntsun da ya ja ruwa, to shi ruwan kan doka, amma kuma ai Hausawa na cewa, wanda ke cikin dakin shi ya san inda shigifa ke yoyo! Sai dai da alama ya Shugaba Buhari, kana zaune a cikin dakin ne, amma ba ka san inda shigifar ke yoyo ba, ko kuma ka sani, ka dai yi bakam ne, kamar sauran ’yan Najeriyar da kake mulka, wato kar ta san kar, ko Ali ne ya ga Ali, ko za-mu-ne ta tarar da mu-je-mu, ba abin da za ka yi, ba kuma abin da wasu za a iya yi kan haka, me ya sa na ce haka?

ADVERTISEMENT

Shin ya Shugabana Muhammadu Buhari ka taba tambayar kanka su wane ne masu tayar da hankalin jama’ar kasar nan kama daga ’yan Boko Haram zuwa ’yan fashi da makami da satar shanu da ta mutane da masu tsare hanya domin kwace da sane a kasuwanni ko kan tituna da karuwanci da madigo da daudanci da yahuzi da karbar hanci da rashawa a ofisoshi da sojoji da ’yan sanda, masu hada baki da wasu ’yaa Najeriya domin a cutar da ’yan Najeriya, wai shin ’yan Najeriya ne ko wasu baki daga waje? Shin ka taba tambayar kanka cewa su wadannan rubabbun ’yan Najeriyar ba su da masaniya cewa muggan dabi’u da sana’o’i da  ayyukan da suke yi suna lalata kasar nan ne, suna musguna wa ’yan kasar nan ne, sa’annan kuma wasu daga cikin su, su ne suka sake zabarka domin ka gyara kasar nan domin a samu sauki?

Shin da gaske irin wadannan gungun al’umma gyara suke so ka yi wa kasar nan? Shin me zai hana su gyaru da kan su, ba sai sun wahalar da tsohon mutane a banza ba? Shin ka taba yin zugum ka tambayi kanka, me ya sa irin wadannan batattun mutane ’yan Najeriya za su bata lokuttansu wajen zabenka a matsayin ‘mai gaskiya’ domin ka gyara lamurran ‘marasa gaskiya? Shin ya Shugabana ba ka jin shi ya sa kullum abubuwa ke kasa yin gaba ko baya a kasar nan, ko abin da Hausawa ke cewa ana gyara irin na gangar Azbinawa?

Shin ya Shugabana Buhari ba ka jin cewa aiki ne ja a gabanka game da wasu daga cikin wadannan matsalolin kasar nan shi ya sa an kasa gaba ko baya? Shin bai dace ba ka gane cewa ’yan Najeriya ba su damu da duk wani kokari da kake yi ba don kawo gyara ko sauyi ko canji, domin su ne matsalar, ba kuma a shirye suke su canza halayensu ba, har Mahdi? Idan har ka fahimci wannan kullin ya Shugabana, to abin da nake so ke nan ya Shugaba Buhari ka sanar da ’yan Najeriya a lokacin da za ka soma zama kan ragamar mulki karo na biyu daga ranar 29 ga watan Mayun 2019. Kai dai mai gaskiya ne, to don Allah ka gaya wa ’yan Najeriya gaskiyar. Fada musu, su ji da kunnuwansu cewa sun zabe ka ne ka kawo canji ga mutanen Najeriya ba aljannu ko mala’iku ko wasu al’umma da ke rayuwa a sararin samaniya ba, ’yan Najeriya fa aka ce! Wato irin su ministocinkla masu yi wa kasa zagon kasa! Ma’aikatan gwamnatoci tun daga Tarayya zuwa Jihohi da ke rayuwa cikin cin hanci da kwanciya cikin rashawa. Malamai da ke amfani da addini domin su azurta kansu. Fada-Fada da wasu irin su masu zuwa Coci domin su cutar ba don su wa’azantar ba. Sarakuna da ke bin dare domin gurgunta rayuwar talakawansu. Masu kudi da tarin dukiyar da sun haukace, sun makance, ba su tu’ammali da komi sai riba da riba, wadanda jari ya fiye musu komi a rayuwa.

Ina ba ka shawara ya Shugaba Buhari, da ka gaya wa talakawan nan da suka zabe ka domin ka kawo sauyi ko canji ko gyara, cewa ka fasa kawo gyaran ko canjin ko sauyin, su talakawan su fito su gyara, ai ba ka fi talakawan son ci gaban kasar ba.

 

Za Mu Ci Gaba

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya