✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fallasa sarakunan da ke hada baki da ‘yan bindiga — ‘Yan Katsina

Mutanen jihar Katsina sun kalubalanci Gwamantin Tarayya da ta fallasa sarakunan da ta ce suna hada baki da ‘yan bindigar da ke addabar jihar.  Jama’ar…

Mutanen jihar Katsina sun kalubalanci Gwamantin Tarayya da ta fallasa sarakunan da ta ce suna hada baki da ‘yan bindigar da ke addabar jihar. 

Jama’ar jihar sun ce muddin Gwamnati taki tona asiri ta kuma tsare sannan ta hukunta sarakunan da ke taimakon ‘yan bindigar da suka kashe daruruwan mutane a jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma ba, to ba komai take yi ba face neman kin daukar laifinta.

Mazauna da iyayen kasa a yankunan da hare-haren ‘yan bindiga suka yi kamari a jihar Katsina sun bayyana wa wakilinmu muhimmacin fallasa miyagun masu sarautar gargajin da ke hada baki da maharan domin kawo karshen matsalar.

Kiraye-kirayen na zuwa ne bayan zargin da Babban Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai Garba Shehu ya yi  ranar Litinin 15 ga watan Yuni.

A hirarsa da gidan talbijin na Channels, Garba Shehu za zargi wasu sarakunan Katsina da hada baki da kuma taimaka wa ‘yan bindiga ta hanyar ba su bayanai su tsere idan sojoji za su kai musu hari.

“Hatta a jihar Katsina inda Shugaban Kasa ya fito, an sami wasu sarakuna da ke hada baki da ‘yan fashin daji a cutar da mutanensu”, inji shi.

‘Yan bindiga na yawan kai hare-hare a yankunan jihar Katsina musamman a makon jiya, inda suka kashe kusan mutum 100 a kauyuka.

A  hirarsa da gidan talbijin na Channels a ranar Litinin inda ya ce miyagu na amfana da ayyukan ‘yan bindigar, Garba Shehu ya ce, “A jihar Zamfara ma sai da aka tube wasu  Sarakuna da hakimai”.

Jami’in ya ce a baya lokacin da abin ya fi kamari a jihar Zamfara, kafin jiragen yaki da aka girke a Katsina su kai wa ‘yan bindiga hari wasu sun kira sun sanar da  su har sun sake wurin buya kafin jiragen su isa.

Ya ce, “Karshenta dole jiragen suka koma tashi daga Kano da Kaduna domin kai wa ‘yan bindiga hari a Zamfara”.

Garba Shehu ya yi kira da a taimaka wa gwamnati ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen magance ayyukan maharan.

“A matsayinmu na ‘yan kasa akwai hakki a kanmu na mu taimaka wa sojoji da bayanai”, inji shi.

— Gwamnatin Katsina ta yi gum

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Abdu Labaran Malumfashi, Mai Magana da Yawun Gwamna Aminu Bello Masari, amma ya ce ba zai yi magana akan lamarin ba. “Ba abin da zan ce,” inji shi.

—Mun ji kunya, mun kasa kare mutanenmu

Wannan juyin wainar na zuwa ne bayan gwamnan jihar ya sanar da janye sulhun da gwamnatinsa ta yi da ‘yan bindigar wadanda ya ce sun ci amanar alkawarin da gwamnatin ta yi da su. A dalilin sulhun ne a baya gwamnatin jihar ta ce ta yi afuwa ga ‘yan bindigar.

A baya-bayan nan Masari ya ce ya amince gwamantinsa ta kasa sauke nauyin da ya rataya a kanta na kare jama’ar jihar, yana mai cewa ba zai iya hada ido da jama’ar yankunan da ‘yan bindigar ke addabarsu ba.

“Zaki ma a daji ba ya kisa sai ya ji yunwa kuma ba ya kashe daukacin dabbobi sai wanda zai iya ci a lokaci guda.

“Amma su ‘yan bindiga suna shigowa gari su yi ta harbin kan mai uwa da wabi suna kisan jama’a ba gaira ba dalili kamar yadda suka yi a baya bayan nan a sassan Faskari da Dandume inda suka yi ta kisan jama’a.

“Don haka na ce hallayarsu ta fi ta dabbobi muni, Ni a ganina babu sauran wani mutumin kirki da ke zaune a daji”, inji shi.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta yi akalla kaso 90 cikin 100 na abun da za ta iya yi, kuma a dokar tsarin mulkin tsaro na hannun Gwamnatin Tarayya.

Akalla mutum 70 ne suka rasa rayukansu a baya-bayan nan a farmakin ‘yan bindiga a jihar Katsina.

A baya an tube wasu masu rike da sarautar gargajiya bisa zarginsu da hannu a harkar garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara mai makwabtaka da Katsina.

—Masarautar Katsina na tattauna batun

Sakataren Masarautar Katsina kuma Sallaman Katsina, Bello Ifo ya ce Masarautar na tattaunawa game da zargin kuma za ta fitar da matsaya nan gaba.

Shi ma wani basarake da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa bai kamata a yi watsi da zargin ba, don haka wajibi ne Masarautar ta fito ta yi bayani.

Wani basaraken ma ya ce, “Wannan babban zargi ne kuma wajibi ne shugabanninmu su fito su yi bincike. Idan ya tabbata, sai a tube duk wanda aka samu da laifi daga sarauta a kuma hukunta shi.

“Cin amana ne ce basarake, ko da kuwa mai unguwa ne ya sayar da jama’arsa saboda abin duniya.

Ya kara da cewa ya kamata Gwamantin Tarayya ta yi hattara wurin yin irin wannan zargi. Maimakon haka, kawai ta yi ta maza ta bayyana gaskiyar lamarin gaba daya ko mutane za su zauna lafiya.

—Su ma sarakunan ‘yan bindigar sun kashe

“Ana maganar sarakuna na hada baki da ‘yan bindiga, wasunsu kuma ‘yan bindigar na kashe su saboda ko a kwanan nan an kashe wani hakimi a Katsina.

“‘Yan bindigar suka kashe shi. Ina ganin abu ne mai wuyar sha’ani da ya kamata a bi a hankali domin kar a birkita ragowar kwanciyar hankali da ake samu a wasu sassun jihar,” inji shi.