Ambaliya: Kananan hukumomin Kano da ke cikin hadari

Kananan hukumomi 20 daga cikin 44 na Jihar Kano na fuskantar babbar barazanar ruwan sama da ambaliya a daminar bana.

Hukumar agaji ta kasa NEMA ta ce rahoton hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) na daminar 2020 a Najeriya ya yi hasashen samun ruwan sama fiye da kima a kananan hukumomin.

Jam’in NEMA a ofishinta na Kano Sunusi Ado ya ce kananan hukumomin jihar da hasashen ya nuna ambaliyar za ta shafa su ne:

Tarauni, Garum Malam, Rimin Gado, Gaya, Gezawa da kuma Gwale. Akwai kuma Shanono, Gabasawa, Gwarzo, Ungoggo, Warawa da  kuma Dawakin Kudu.

Sauran su ne Dambatta, Bebeji, Kabo, Wudil, Kura, Nassarawa, Kumbotso da kuma Karamar Hukumar Birni.

Sanusi Ado ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan wayar da kai da aiwatar da rahoton hasashen ruwan sama na 2020.

Ya ce ruwan da za a samu a damunar bana zai haura yadda aka saba samu, wanda hakan ya sa wasu wurare a cikin hadarin ambaliya.

Jami’in ya kuma jaddada bukatar wayar da kai game da daukar matakan da suka dace mutane su bi domin taimakawa a dakile barazanar ambaliya ta hanyar yin kyakkyawan shiri.

Da yake mayar da jawabi, Babban Sakataren hukumar agaji ta jihar Kando (SEMA) Saleh Aliyu Jilli ya ce hukumomin biyu na aiki tare domin shawo kan matsalar yadda ya kamata.