✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An girke jami’an tsaro bayan barkewar rikici a Jos

An fasa shaguna da gilasan motoci tare da kone-kone bayan ballewar rikici a Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta girke jami’an tsaro domin dakile yiwuwar ballewar rikici a sassan garin Jos.

An girke ‘yan sandan a sassan garin bayan rikici ya balle a wurin zanga-zangar #EndSARS da safiyar Talata.

Masu rikicin sun farfasa shaguna da gilasan motoci tare da kone-kone a garin na Jos.

Tarzomar ta tashi ne bayan wasu matasa sun tare Titin Ahmadu Bello da ke garin a ci gaba da zanga-zangar #EndSARS ta kin jinin cin zalin da ‘yan sanda ke yi.

Wasu matasa da tare hanyar bai yi musu dadi ba suka kalubalanci hakan, lamarin da ya tayar da husuma a tsakaninsu.