✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gwabza fada tsakanin jami’an Kwastam da ‘yan kasuwa

Mutane da dama ne suka jikkata biyo bayan wata arangama tsakanin jami’an hukumar hana fasakwabri ta kasa (Kwastam) da ‘yan kasuwar bajekoli ta kasa wato…

Mutane da dama ne suka jikkata biyo bayan wata arangama tsakanin jami’an hukumar hana fasakwabri ta kasa (Kwastam) da ‘yan kasuwar bajekoli ta kasa wato kasuwar ‘Trade Fair Complex’, da ke Ojo, a Legas.

Jami’an hukumar ta Kwastam wadanda soji suka rufa wa baya sun dirar wa kasuwar ne biyo bayan bayanan sirri da suka samo na shigar da kayayyakin fasakwabri daga kasar Benin ta kan iyakar tudu ta Same boda zuwa cikin Najeriya.

Jami’an Kwastam din sun gamu da turjiya daga ‘yan kasuwar ne wadanda suka ce, sam baza a binciki runfunar kasuwarsu ba, inda suka yi ta jifan jami’an da duwatsu har sai da shugabannin kasuwar suka shiga tsakani.

Majiyar mu ta samu rahoton cewa, jami’an Kwastam din sun kwashi kayayyaki da dama daga cikin kasuwar, musamman a manyan shagunan saye da sayarwa na Jigawa complex da Adamawa Plaza da suka hadar da shinkafa waje da man girki.

Dokar kasa ta bai wa jami’an Kwastam hurumin shiga ko ina domin yin bincike tare da kame kayan fasakwabri ba tare da sun bukaci takardar sammaci daga kotu ba, dokar da ake wa lakabi da CEMA (Customs Excise Management Act CEMA) a takaice.