✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama fasto kan safarar yaran Arewa zuwa kudancin Najeriya

Asirinsu ya tonu bayan sun kwaso yaran masu shekaru 5 zuwa 16 daga Jihar Nasarawa zuwa wani wuri Jihar Ogun.

’Yan sanda a Abuja sun kama wani fasto da wasu mutane biyu bisa zargin safarar kananan yara daga Jihar Nasarawa zuwa Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a bayan da da farko ’yan sandan sun kama wani direban wata motar haya dauke da yaran 12, maza hudu da mata takwas.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce an kwaso yaran masu shekaru 5 zuwa 16 ne daga Akwanga  a Jihar Nasarawa zuwa wani wuri da aka gano daga baya cewa Jihar Ogun ne.

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa dukkan yaran sun fito ne daga Karamar Hukumar Akwanga, kuma wani Fasto Simon Kado da Jesse Simon Kado da yanzu haka suna hannun ’yan sanda ne ke safarar su.

“Kuma yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, rundunar tana kokarin ganin ta mika wa rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa yaran domin hada su da iyalansu,” in ji shi.

CP Benneth Igweh ya jaddada aniyar rundunar wajen tabbatar da tsaron al’umma, sannan ya yi kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ba su aminta da shi ba ga lambobin kar-ta-kwana na rundunar: 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; 09022222352.