✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: An yanke wa mawaki hukuncin rataya

Za a rataye matashin da ya yi wa Manzon Allah (SAW), an kuma daure wani shekara 10

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifin batanci da Manzon Allah (SAW).

Kotun Mai Shari’a Muhammad Ali Kani ta kama matashin mai suna Yahaya Sheriff Aminu da laifin kaskantar da darajar Manzon Allah (SAW) a wani sakon muryarsa da ya yada.

Ya kuma yanke wa wani matashi da ya yi batanci ga Allah daurin shekara 10 tare da aiki mai tsanani a kurkuku, saboda karancin shekarunsa.

An gurfanar Yahaya, mai kimanin shekaru 30 dan asalin Unguwar Sharifai a Kano, da yada wakar da a ciki ya yi batancin ga Manzon Allah (SAW) ta wani zauren sada zumunta na Whatsapp mai suna ‘Gidan Ummu Abiha’.

Mai Shari’ah Muhammad, ya ce Yahaya, wanda dan Faila ta Darikar Tijjaniya ne, na da kwana 30, da zai iya daukaka kara.

A ranar 22 ga Fabrairu, 2020, aka fara gurfanar da Yahaya a kotun, inda mai gabatar da kara, Insfekta Aminu ‘Yargoje ya shaida wa kotun cewa Yahaya ya fifita Shaikh Ibrahim Nyass a kan Annabi Muhammad (SAW).

— Tijjaniyya ta nesanta kanta da mawakin

Tun a lokacin da Yahaya ya fitar da wakar, kungiyar ‘yan Tijjaniya ta Jam’iyyatu Ansariddeen ta barrantar da kanta daga mawakin saboda wakar tas batanci ne ga Manzon Allah.

Sakataren Kungiyar na Kasa, Sayyidi Muhammad AlQasim Yahaya a cikin watas sanarwa ya ce Darikar Tijjaniya da Shaikh Ibrahim Nyass na duk masoyan Manzon Allah ne.

Wakar da matashin ya yi ya kuma yada a shafukan zumunta ta fusata mutanen Kano, wandanda suka ce tsagwaron cin mutunci ne ga Annabi (SAW).

A wancan lokaci daruruwan fusatattun jama’a suka yi wa gidansa tsinke, suka farfasa shi tare da kokarin rushe shi da kone shi.

— An yi zanga-zangar la’antar matashin

Kazalika a lokacin da wakar batancin ta fita, wadansu mutane a karkashin jagorancin wani mai suna Malam Alkassim Abdullahi sun gudanar da zanga-zangar lumana ta neman hukuma ta dauki mataki a kan Yahaya Sharif Aminu.

Daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano inda suka samu tarba daga Kwamandan Hukumar Sheikh Sani Ibn Sina da wakilin Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Habu Sani da kuma DPO na Gwale da na cikin birni.

Musulmi a lokacin da suke zanga-zangar la’antar cin zarafin Annabi da matashin ya yi a Kano
Musulmi a lokacin da suke zanga-zangar la’antar cin zarafin Annabi da matashin ya yi a Kano

A cikin jawabin da ya gabatar, Malam Alkasim ya ce abun da matashin ya yi cin mutunci ne ga addinin Musulunci wanda ya kamata kowane Musulmi ya yi tir da shi.

A lokacin ya yi kira ga shugabannin da su gaggauta kamo matashin don ya fuskanci hukuncin laifin da ya aikata don ya zama izna gare shi da na baya.

A jawabansu, Kwamandan Hukumar Hisbah da wakilin Kwamishinan ’Yan sandan sun ba masu zanga-zangar tabbacin cewa za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin wanda ake zargin ya zo hannu tare da gurfanar da shi gaban shari’a.

Haka kuma sun ja hankalin jama’a kan illar daukar doka a hannu inda suka neme su da bin matakin shari’a a duk lokacin da abubuwa makamancin wannan suka taso.

— Ba wannan ba ne na farko

Wannan ba shi ne karon farko da ake samun masu yin batanci ga Annabi (SAW) a Kano ba.

A shekarar 2015, wani mai suna Abdul Nyass ya aikata makamancin irin wannan batanci, wanda sakamakon haka gwamnatin jihar ta gurfanar da shi a kotu.

Gwamnatin jihar ta gurfanar da wata Maryam Sayyada da wadansu mukarrabanta a gaban Kotun Lardi ta Shari’a da ke Rijiyar Lemo bayan da Abdul Nyas wanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki ya gudu daga Kano sakamakon hargitsin da kalamansa ga Annabi (SAW) suka jawo.

Daga bisani jami’an tsaro sun kama Abdul a Abuja kuma aka dawo da shi Kano domin fuskantar sharia’a.

Bayan da aka dawo da shi Kano, an gurfanar da shi a gaban Kotun Lardi ta Shari’a da ke Rijiyar Lemo inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai Abdul Nyass ya daukaka kara zuwa Babbar Kotun Kano domin kalubalantar hukuncin da Kotun Shari’ar ta yanek a kansa.

Amma lokacin da Alkalan Kotun biyu, Mai shari’a Yusuf Muhammad Ubale da Hadiza Sulaiman suka saurari karar, sun tabbatar da hukuncin da Kotun Shari’ar ta yanke masa.

Abdul Nyas ya sake daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke  Kaduna.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kotun ta Kaduna ba ta fara sauraron karar Abdul Nyas ba.

Ana samun matasa a baya-bayan nan da suke alakanta kansu da Faila -Tijjaniyya da suke wuce gona da iri wajen yabon marigayi Shehu Ibrahim Nyass, inda a karshe suke kaiwa ga cin zarafin Annabi (SAW).

Wannan ya sa wadansu daga cikin malaman Tijjaniya ’yan Failar suka fara barranta daga wadannan matasa.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda hankalin daya daga cikin limaman Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya tashi har ya bayar da fatarwar a rika  kashe masu aikata haka.