✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sake nada Mahmud Yakubu a matsayin shugaban INEC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Mahmud Yakubu a matsayin shugaban (INEC)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nada shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar a karo na biyu.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina wanda ya tabbatar da hakan da yammacin ranar Talata ya ce Buhari ya sanar da sake nadin ne a wata wasika da ya aikewa da shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Buhari ya ce nadin ya dace da tanade-ranaden sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyaran fuska.

“Ina farin cikin gabatar da sunan Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban INEC a karo na biyu domin neman amincewarku,” inji shugaban a cikin sanarwar da kakakin nasa ya wallafa.

Farfesa Mahmud dai ya dare shugabancin hukumar ne a 2015 kuma zai shafe karin wa’adin wasu shekaru biyar nan gaba matukar Majalisar ta amince da bukatar shugaban ta sake nada shi.