✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China ta gargadi shugabannin masu zanga-zanga a Hong Kong

Kasar China ta yi gargadi mai tsauri ga masu neman canji wadanda suka janyo harkoki a Hong Kong suka tsaya cik, bayan sama da wata…

Kasar China ta yi gargadi mai tsauri ga masu neman canji wadanda suka janyo harkoki a Hong Kong suka tsaya cik, bayan sama da wata biyu da suka yi suna gudanar da zanga-zanga mai zafi.

Yang Guang, Kakakin Hukumar Harkokin Hong Kong da Macao, ya fada wa manema labarai yayin wani taron tattaunawa a Beijing cewa “Lokaci dan kalilan ya rage, kafin shugabannin masu zanga-zangar su fuskanci hukunci.”

Makonni da dama da aka yi ana gudanar da zanga-zanga a kan tituna, sun jefa cibiyar hada-hadar kudade ta Asiya cikin mummunan rikicin siyasa, wanda ba a ga irinsa ba tun lokacin da Birtaniya ta mika mulkin yankin ga kasar China a 1997.

Zanga-zangar an fara ta ce a watan Yuni bayan mazauna garin Hong Kong suka fusata da kudirin dokar mika masu aikata laifuffuka ga China don su fuskanci hukunci.

A sanadin wannan tashin hankali aka dakatar da dokar, amma zanga-zangar ta ci gaba kuma tuni ta juye zuwa kira ga neman a canja fasalin mulkin yankin.