✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An raba wa talakawa kudi

Gwamnatin Najeriya ta fara raba wa marasa galihu da ke Yankin Babban Birnin Tarayya N20,000 ko wanne don rage masu radadin dokar da aka ayyana…

Gwamnatin Najeriya ta fara raba wa marasa galihu da ke Yankin Babban Birnin Tarayya N20,000 ko wanne don rage masu radadin dokar da aka ayyana ta hana fita a yankin.

Wadanda za su ci moriyar tallafin dai marasa galihu ne a yankin su 50,000 wadanda ke karkashin tsarin gwamnati na bayar da N5,000 duk wata bisa sharadi.

A jawabin da ya yi ranar Lahadi na ayyana dokar ta hana fita, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya bayar da umarni a bai wa wadannan mutane kudin su har na watanni biyu nan take.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwato Ministar Ayyukan Jinkai da Agajin Gaggawa Hajiya Sadiya Umar yayin kaddamar da aikin a karamar hukumar Kwali tana cewa matakin bin umarnin shugaban kasa ne.

“Naira 5,000 ake bai wa masu cin gajiyar wannan tsari duk wata; don haka N20,000 din da za a bai wa ko wanne yanzu na wata hudu ke nan.

“Haka za a yi a fadin kasar nan, amma za mu fara da Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun ne saboda su ne kan gaba [a yaki da annobar coronavirus]”, inji Hajiya Sadiya.

Da ma dai ga alama ba a bai wa mutanen kudin tallafin na watannin Janairu da Fabrairu ba.

Daya daga cikin wadanda suka karbi kudin, wata uwa mai ‘ya’ya biyu, Misis Sarah Gadaga, ta ce ta yi farin ciki.

“Ba mu kudin na watannin Janairu da Fabrairu da Maris da Afrilu, wanda ya kama N20,000, zai taimaka min na bunkasa harkar kasuwancina, na biya kudin makarantar yara da ake bi na, na kuma biya sauran bukatu na gida”.

Ranar Lahadi ne dai Shugaba buhari ya bayar da umarnin hana fita har tsawon mako biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun a matsayin wani mataki na kawo karshen yaduwar COVID-19.