✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Almajiran da ke ‘karyawa da kwai’ sun yi yunkurin tserewa

Daruruwan almajiran da aka killace a wani sansanin masu yi wa kasa hidima a jihar Jigawa sun yi yunkurin tserewa. Almajiran da gardawa da ma…

Daruruwan almajiran da aka killace a wani sansanin masu yi wa kasa hidima a jihar Jigawa sun yi yunkurin tserewa.

Almajiran da gardawa da ma alarammomi sun yi zanga-zanga ne ranar Juma’a, suna zargin cewa ba a ba su kulawar da ta dace.

Da yake yi wa kwamitin yaki da cutar coronavirus na Jigawa bayani a kan lamarin, daya daga alarammomin da ke sansanin, Malam Hamisu Alaramma, ya ce akwai matsalar rashin samun abinci a kan lokaci.

Malam Hamisu ya kara da cewa wani lokaci ba a ba su abinci sai karfe 10.00 ko 11.00 na safe, alhali a cikinsu akwai yara kanana wadanda ba sa azumi.

‘Da kwai suke karyawa…’

Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Abba Zakari Umar, ya garzaya sansanin ne bayan da ya samu bayanin gaggawa game da halin da ake ciki daga jami’an tsaro.

Sai dai daga bisani kwamishinan ya musanta cewa ba a kula da almajiran da alarammominsu yadda ya kamata.

Ya ce gaskiya ne yaran sun yi zanga-zanga, amma “saboda sun zaku suna son su tafi gida.

“Hakan ya biyo bayan fitowar sakamakon wasu daga cikinsu, inda aka sallami wasu”, inji shi.

Da wakilinmu ya tambaye shi game da zargin da almajiran suka yi cewa ba a kula da su ta bangaren abinci, sai kwamashinan ya ce: “Ku daina kawo mana fitina a cikin aikinmu; mu a iyaka saninmu muna ba su abinci da kulawar da ta dace.

“Sau da yawa yaran ma da kwai suke karyawa”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “mu ba mu san dalilin da ya sa yaran nan suke son ficewa daga sansanin ba, amma mun zauna da malamansu mun tattauna a kan matsalar an shawo kanta”.

Almajirai 16 sun kamu

A halin da ake ciki kuma, daga cikin almajirai 45 da aka tura sanfurinsu Abuja don gwaji an gano 16 na dauke da cutar coronavirus.

Wadannan dai suna cikin almajiran da jihar Kano ta dawo da su a kwanakin baya su 607.

Dokta Abba Zakari Umar ya ce yanzu haka akwai almajirai 29 da aka tabbatar ba sa dauke da cutar bayan gwajin da aka yi masu.

Saboda haka, a cewar shi, gwamnatin jihar ta umarci a bai wa ko wanne almajiri N10,000, da kayan sawa sababbi, a kuma dauke shi a kai shi gaban mahaifansa.

Ya kara da cewa yanzu haka ana jiran sakamakon almajirai 550 wadanda aka tura da samfurinsu Abuja don tabbatar da lafiyarsu daga cikin almajiran da aka dawo da su daga Kano.

Ana killace da almajirai 1,114 

Ya ce almajirai 16 da aka samu da cutar kuma za a ci gaba da killace su a cibiyar da aka tanada a hedkwatar jihar domin ci gaba da duba lafiyarsu.

Da yake karin haske a kan adadin almajiran da Jigawa ta karba daga jihohin Kano, da Kaduna da Gombe da Nasarawa, ya ce yanzu haka jihar tana da almajirai 1,114 wadanda take ajiye da su a sansanin na masu yi wa kasa hidima da ke Fanisau.

Ya ce ana ran samun karin almajirai 89 daga jihar Filato ranar Juma’a wadanda ya ce da zarar sun zo za a killace su na tsawon mako biyu.

“Su ma za a dauki samfurinsu a tabbatar da lafiyarsu kafin a mika su ga iyayensu”.

Gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya ne dai suka amince su mayar da almajiran da ke yankunansu garuruwansu na asali, matakin da ya sha suka har ma daga gwamnatin tarayya.