Search
Subscribe
Coronavirus: Mutum 10 sun kamu rana guda bayan barazanar dokar kulle

Gwamnan Osun Adegboyega Oyetola

Coronavirus: Mutum 10 sun kamu rana guda bayan barazanar dokar kulle

Wasu sabbin mutum 10 sun kamu da cutar coronavirus a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni a jihar Osun.

‘Yan kwanaki ke nan da gwamnatin jihar ta ce za ta dawo da dokar kulle muddin yaduawr cutar ta kara kamari a jihar.

Kwamishinan Lafiyan Jihar, Rafiu Isamotu ya ce kamuwar sabbin matanen ya sa adadin masu cutar a halin yanzu kaiwa 64.

“Da abin da ya faru yanzu, mutum 64 ke fama da cutar zuwa yau Lahadi, 28 ga watan Yuni”, inji shi.

Da yake gargadin jama’ar jihar da su gudi jita-jita game da cutar a jihar, Kwamishinan ya bukace su da su bayar da hadin kai domin a yi nasara a yiki da cutar a jihar.

“Gaba daya mutum 116 ne suka kamu, daga cikinsu mutum 47 sun warke bayan an yi musu magani, sai mutum biyar ta suka rasu”, inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin