✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kashe likita a Jigawa

Annobar coronavirus ta yi ajalin wani likita a Karamar Hukumar Birnin kudu dake jihar jigawa. Kungiyar Likitocin Najeriya reshen jihar Jigawa ta sanar da rasuwn…

Annobar coronavirus ta yi ajalin wani likita a Karamar Hukumar Birnin kudu dake jihar jigawa.

Kungiyar Likitocin Najeriya reshen jihar Jigawa ta sanar da rasuwn Dr Nasir Adam ta dalilin cutar.

Malam Nura Basirka na reshen kungiyar  ya ce Dr Nasir ya rasu a bakin aiki bayan kamuwa da cutar yana da shekaru 36 a duniya.

Kungiyar ta ce an tabbatar da rasuwar Dr Nasir ta dalilin cutar coronavirus ne  ta hanyar gwaje-gwaje da likito su ka yi masa.

• Coronavirus: mutum 800 ne za su iya kamuwa a Jigawa

• An dage dokar kulle saboda Sallar Idi a Jigawa

Dr Basirka ya ce mamacin ya rasu  sakamakon sarkewar nunfashi wanda daga bisani aka gano cewar cutar coronavirus ce.

Marigayi Nasiru Adam ma’aikaci ne cibiyar lafiya ta tarayya da ke Birnin Kudu kamar yadda dakta Basirka ya tabbatar.

Aminiya ta yi bayanin yadda ma’aikatan lafiya a jihar Jigawa suka kamu da cutar ta coronavirus kuma suka Sami sauki.