✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya kai 174

A karo na biyu a ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun karin mutunen da suka kamu da cutar coronavirus. Sababbin alkaluman…

A karo na biyu a ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun karin mutunen da suka kamu da cutar coronavirus.

Sababbin alkaluman dai sun nuna cewa an samu karin mutum 23; abin da ya kai adadin wadanda aka tabbatar a Larabar kadai zuwa 35.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta bayyana cewa a yanzu yawan wadanda aka tabbatar sun kamu ya haura 170.

“Zuwa karfe 8.00 na daren 1 ga watan Afrilu, an samu mutum 174 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19.

“Daga cikin wannan adadi an sallami mutum tara, yayin wasu mutum biyu suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.

Abba Kyari na murmurewa —Kwamishinan Lafiya

Wadanda suka cancanci gwajin Coronavirus

A yanzu dai jihar Akwa Ibom ta shiga jerin jihohin da aka samu wadanda suka kamu, da mutum biyar.

Tara daga cikin sauran sabbin kamun dai a Legas suke, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Kaduna, daya a Bauci.