✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An samu sabbin kamuwa 22

An samu karin mutane 22 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce…

An samu karin mutane 22 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

An samu 15 daga cikin mutanen 22 ne a jihar Legas, hudu a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a jihar Bauchi, daya kuma a jihar Edo.

“Zuwa karfe 9.00 na daren 8 ga watan Afrilu, an samu mutum 276 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji NCDC.

“Daga cikinsu an sallami 44, yayin da shida suka riga mu gidan gaskiya”.

A ranar Talata ne dai aka sanar da mutum na farko da aka tabbatar da ya kamu da cutar, kuma na farko da ta yi ajalinsa a jihar Katsina.