✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Masu kasa da 5,000 a banki za su ci moriyar tallafin gwamnati

Gwamnatin tarayya ta ce, mutanen da suka mallaki abin da bai kai Naira dubu biyar ba, a asusun ajiyarsu na banki suna cikin nau’i uku…

Gwamnatin tarayya ta ce, mutanen da suka mallaki abin da bai kai Naira dubu biyar ba, a asusun ajiyarsu na banki suna cikin nau’i uku na mutanen da wadanda za su ci gajiyar umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na raba tallafi don rage wa talakawa radadin matakan yaki da COVID-19.

Ministar Al’amuran Jinkai da Agajin Gaggawa Sadiya Umar Farouq, ce ta fadi haka a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Hajiya Sadiya, wacce ta bayyana cewa a yanzu ma’aikatarta za ta fi mayar da hankali ne ga matalautan da ke birane wajen aiwatar da umarnin na shugaban kasa, ta kuma ce akwai hanyoyi uku da za a iya bi don zabo mutum miliyan dayan da shugaban kasa ya ce a kara a kan wadanda ke samun tallafi a baya.

“Kuna sane cewa, a jawabinsa na ranar Litinin 13 ga watan Afrilu, shugaban kasa yaba da umarni cewa, a fadada rajistar wadanda ke amfana da gudunmawar kudi bisa sharadi da mutum miliyan daya, don haka za mu fi mayar da hankali ga matalautan da ke birane.

“Wadannan mutane ne wadanda suka dogara da aikin hannu don samun abin da za su ci; su ne wadanda sai sun fita a kullum suke samun na kashewa kuma su ne mutanen da za mu fi ainihin mayar da hankali gare su da ma nakasassu.

A nan muna da zabi uku: na daya za mu yi amfani da rajistar da da ma muke da ita, na biyu za mu mayar da hankali ga matalautan da ke birane kamar yadda na fada, ta hanyar amfani da lambar tabbatar da sahihancin asusun ajiyarsu na banki wato BVN—ma’ana mutanen da ke suka mallaki N5,000 a asusunsu na banki ko kasa da haka.

“Za kuma mu hada hannu da kamfanonin wayar salula, don sanin mutanen da kudin da suke zubawa a wayoyinsu bai haura N100 ba. Wadannan ne mutanen da muke dauka talakawa masu rauni….

“Bari kuma nace muna da iyaka. Kashi 25 cikin 100 na al’umma kadai za mu iya tallafawa don abin da muke da shi ba zai isa kowa ya samu ba—don haka za mu fara da kashi 25 na al’ummar wuri.

Misali kashi 25 na al’ummar jihar Legas ne kawai za su amfana da wannan tallafi; akwai yiwuwar nan gaba mu kara, amma abin da ya samu ke nan a yanzu”, inji Ministar.

`Sai dai kuma wasu ‘’yan Najeriya na sukar wannan shawara suna masu cewa galibin talakawa ba su da asusun ajiya a banki basu kuma da wayar salula.