✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya gana da Majalisar Sarakuna

Ganawar ta zo ne a ranar da El-Rufai ya ce zai yi wa masarautar gyaran fuska

Gwamnan Jihar Kaduna ya shafe awanni yana ganawa da Majalisar Sarakunan bayan gabatar da kasafin kudin jihar na 2021.

A wurin gabatar da kasafin a zauren majalisar a ranar Talata ne gwamnan ya ce yana shirin gabatar mata da kudurin dokar gyaran fuska da tsarin masarautu da majalisar sarakunan Jihar.

Har zuwa Magariba, gwamnan bai gama taron da Majalisar Sarakunan ba wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Samuel Aruwan ya halarta,  kamar yadda wakilinmu ya shaida mana.

A ranar ce gwamnan yana shirin gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kudurin Dokar yi wa tsarin masarautu a jihar gyarar fuska.

El-Rufai yayin gabatar da kasafin kudin 2021 a zauren majalisar ya ce, “Za mu kawo wa Majalisa karin kudurorin doka domin karfafa shugabanci a jihar

“Hakan zai kawo gyare-gyare a hakimci da sarauta zai kuma kayyade abin da masarautu za su kunsa da rabe-rabensu tare da zamantar da tanade-tanaden masarautu da dokokin da aka gada daga turawan mulkin mallaka”

Sabuwar dokar ta za ta kawo sauye-sauye ga tsarin sarauta da kuma hakimci a masarautun jihar.

Bayanin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin yana shirin kirkirar karin masarautu biyu daga Masarautar Zazzau.

Ana hasashen gwamnan zai karkasa Masarautar Zazzau ta yanzu zuwa masarautu uku ne domin gidaje uku da ke kan gaba wajen neman gadar kujerar Sarautar Zazzau su samu sarauta.

Bisa sabon tsarin da ake hasashe, Masarautar Zazzau za ta koma masarautu uku da suka hada da Zariya, Kudan da kuma Kaduna.

Yariman Zazzau ne zai zama Sarkin Zariya, Iya Zazzau zai zama Sarkin Kudan sai kuma Magajin Gari ya zama Sarkin Kaduna.

Tun a ranar 10 ga watan Satumba, 2020 Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris rasuwa bayan shekara 45 yana sarauta.

Tun bayan rasuwarsa ake ta kwan-gaba-kwan baya kan nada sabon sarki tsakanin Masu Zabar Sarki na masarautar da Gwamnatin Jihar.

A makon jiya ne gwamnan ya umarci Masu Zabar Sarkin Zazzau su biyar da su yi watsi da su yi watsi da sunayen masu neman sarautar Zazzau ta 19 da suka mika masa su sake sabo.

Kujerar Sarkin Zazzau ita ce mafi girma a Jihar Kaduna inda kananan hukumomi 11 daga cikin 28 na jihar ke karkashinta.

Kananan Hukumomin da ke karkashin Masarautar Zazzau sun hada da Zaria, Sabon Gari, Giwa, Kudan, Makarfi, Ikara, Kubau, Soba, Igabi, Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu.