✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: An cafke ‘barayi’ 238 da taraktoci 35 a Adamawa

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun cafke mutum 238 bisa zargin satar kaya a rumbunan ajiyar gwamnati da na jama’a. Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar, Olubenga…

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun cafke mutum 238 bisa zargin satar kaya a rumbunan ajiyar gwamnati da na jama’a.

Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar, Olubenga Adeyanju, ya nuna wa ’yan jarida kayan da aka kwato daga wurin mutanen da suka hada da taraktoci 35, garemanin tarakta 22, taraktocin hannu 28, babura masu kafa uku 12 da kuma motoci tara.

“A yanzu, muna da maza da mata 238 a jihar da aka kama saboda fasawa da kuma satar kaya a rumbunan gwamnati, kamfanoni da ’yan kasuwa, sai kuma mutum 54 da suka karta dokar hana fita ta gwamnatin jihar”, inji Kwamishinan ’yan sandan.

Ya ce ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun fara sintirin hadin gwiwa don tabbatar da aminci da dakile zauna-gari-banza daga kai wa dukiyoyin jama’a farmaki a jihar.

Rikici ya fara a jihar ne ranar Lahadi, bayan dandazon matasa sun mamaye dakunan ajiyan gwamnatin jihar a Yola, suka kwashe abincin tallafin COVID-19 da aka ba jihar raba wa mutane.

Daga nan sai fasa wuraren ya yadu zuwa sauran rumbunan ’yan kasuwa, kamfanoni da na ma’aikatun gwamnati a jihar.