Gaskiya ne ba mu biya ‘yan N-Power 12,000 hakkokinsu ba —Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta amince cewa har yanzu ba ta biya akalla matasa 12,000 da ke cikin shirinta na N-Power hakkokinsu na tsawon watanni uku ba.

Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar-Farouk ce ta bayyana hakan ranar Litinin yayin jawabin hadin gwiwa karo na 45 da Kwamitin Kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da annobar coronavirus ya gabatar a Abuja.

Ta ce tsaikon yana da nasaba ne da al’amuran gudanarwa a ma’aikatar.

Ministar ta ce ma’aikatarta na aiki kafada-da-kafada da Ofishin babban akanta na tarayya wajen tabbatar da shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci.

“Iyakar abin da na sani shi ne mun biya dukkan matasan da ke cikin shirin N-Power wadanda aka tantance kuma aka amince a biya su. Akwai matasa 500,000 a cikin shirin”, inji Sadiya.

Ta kuma ce, “Muna nan muna aiki da ofishin Babban Akanta na Tarayya don duba wadanda suke korafin har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba.

“Mun sami ‘yar tangarda ne sakamakon canza tsarin da muke amfani da shi wajen biyansu tun da farko zuwa tsarin biya na GIFMIS a yanzu. Saboda haka matsalar gudanarwa ce da muka fuskanta ta kawo mana tsaikon.

“Akwai masu irin wannan matsalar kimanin 12,000, kuma yanzu haka da nake bayani Babban Sakataren ma’aikatarmu yana Ofishin Babban Akanta na Tarayya don shawo kan matsalar. Da zarar sun kammala binciken, za mu sanar da ku”, a cewar ministar.