✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamnoni sun yi kasadar yin sulhu da ‘yan bindiga’

Gwamnonin Arewa maso Yammacin Najeriya sun yi babbar kasada a sulhun da suka yi da ‘yan bindiga a jihohinsu. Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sanda…

Gwamnonin Arewa maso Yammacin Najeriya sun yi babbar kasada a sulhun da suka yi da ‘yan bindiga a jihohinsu.

Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sanda Ambrose Aisabor, ya ce matakin da kuma “rashin gaskiya” da ke cikin afuwar ne suka sa hare-haren ‘yan bindidgar ke kara ci gaba a yankin.

Ambarose Aisabor ya ce sasantawa da ‘yan bindiga babban kuskure ne, “ga shi yanzu sasancin da suka saya da kudi ya ruguje”, inji shi.

A zantawarsa da wakilin Aminiya game da matsalolin tsaro da suka hadar da karuwar hare-haren Boko Haram da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga, Ambrose Aisabor ya ce wajibi ne a gaggauta daukar kwararan matakai domin magance matsalolin tsaron da ke neman mayar da Najeriya tamkar kasar da babu doka.

A cewarsa ba abin kunya ba ne ga Najeriya ta nemi taimako daga kasashen ketare domin magance matsalolin tsaro, kuma yanzu ne lokacin da ya fi dacewa ta yi hakan.

Aisabor wanda ya ce babu gaskiya a batun ‘gamawa ko kassara’ kungiyar Boko Haram, ya ci gaba da cewa ya kamata Najeriya ta sauya dubarunta na yaki.

“Hukumominmu na tara bayanan sirri sun yi barci. Sauya salon yaki da Boko Haram ke yi ya nuna sun fi dakarun gwamanti tsari”, inji shi.

“Hafsoshin tsaro sun yi iya kokarinsu. Sai a yaba musu a sallame su, sannan a kawo masu sabbin dabaru.

“Ita kuma gwamnati ta yi nazarin irin kudaden da take kashewa a kan tsaro sannan ta gani ko kalliya na biyan kudin sabulu.

“Yanzu ne da ya kamata a nemi taimakon kasashe, ba abin kunya ba ne, inji shi.