✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya lakume rayuka 7 a Binuwai

Mutum biyar ’yan gida daya da karin wasu biyu sun mutu bayan wata babbar mota ta afka wa wata karamar motar haya da ke dauke…

Mutum biyar ’yan gida daya da karin wasu biyu sun mutu bayan wata babbar mota ta afka wa wata karamar motar haya da ke dauke da fasinjoji a garin Gbatse na Karamar Hukumar Ushongo ta Jihar Binuwai.

Shaidu sun ce bayan mamatan sun hau motar za su tafi garin Gboko ne babbar motar ta kwace daga hannun matukinta ta danne su tare da kashe su a nan take.

Rahotanni sun ce malaman Jami’ar Mkar dake Gboko, Joseph Leva da Moses Tarnongo, matarsa da ’ya’yansa uku na daga cikin wadanda suka mutu a hatsarin motar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar Binuwai, Aliyu Baba ya ce mutum bakwai ne suka rasu a hatsarin, yayin da daya kuma ya samu rauni.

Gwamnan Jihar, Samuel Ortom ya jajanta wa Hukumar Gudanarwa, Ma’aikata da daliban Jami’ar ta Mkar bisa rashin malamanta a hatsarin.

Gwamnan ta bakin kakakinsa, Terver Akase ya bayyana lamarin a matsayin mai sosa rai tare da umartar hukumomin da abin ya shafa kan su gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar sa.