✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen sun ba mu kudade —Masu Zanga-zangar #EndSARS

Kungiyar da ke kan gaba wajen shirya zanga-zangar #EndSARS a Najeriya ta bukaci masu zanga-zangar da su hakura su zauna a gida. Kungiyar Feminist Coalition…

Kungiyar da ke kan gaba wajen shirya zanga-zangar #EndSARS a Najeriya ta bukaci masu zanga-zangar da su hakura su zauna a gida.

Kungiyar Feminist Coalition ta shafukanta na sada zumunta, ta yi fatar a kawo karshen tattakin da matasa shafe sati biyu suna yi a fadin kasar, wadda daga bisani ta koma tarzoma musanman a Jihar Legas da wasu jihohin kasar.

A sanarwar kungiyar ta ce ba za ta sake karbar wata gudummawar kudi da sunan #EndSARS ba, sannan ta bukaci matasan da su bi dokar hana fita da aka saka a wasu jihohi.

Ta bayyana cewa ta tara kimanin Dalar Amurka 400,000 na gudummawa daga sassan duniya, kuma har yanzu ba a kashe kudaden ba.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ne bayan sa’o’i da jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis.

Buhari, a jawabinsa, ya bukaci matasa su dakatar da zanga-zangar ta #EndSARS, saboda ci gaba da gudanar da ita “zai jawo wa tsaron kasa matsala kuma ba zai lamunci hakan ba”.