✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa ɗan Chinan da ya kashe Ummita hukuncin rataya

Kotun ta samu ɗan Chinan da laifin kashe budurwarsa UmmuKulthum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller ta yanke wa ɗan Chinan nan, Mista Geng Quangrang hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkashin Kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya yanke hukuncin bayan samun ɗan Chinan da laifin kashe budurwarsa, UmmuKulthum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

A yayin da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Ma’aji ya bayyana cewa yana roƙon wa ɗan China afuwa daga Gwamnatin Jihar Kano.

Masu ƙara karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi, sun shaida wa kotun cewa a ranar 16 ga Satumba, 2022 Mista Geng ya yi amfani da wuka ya riƙa caka wa Ummulkusum Sani a gidansu da ke unguwar Janbulo a Jihar Kano.

“Hakan ya sa aka garzaya da ita asibiti inda likita ya tabbatar da rasuwarta.”

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, masu ƙarar sun kuma gabatar wa kotun hujjoji huɗu yayin da lauyan kariya ya gabatar da hujjoji biyar.

Lauyan Mista Geng, Barista DanAzumi Muhammad, ya nemi kotun ta yi wa wanda yake karewa sassauci wajen hukunci.

Ya kuma bayyana cewa wanda ake ƙara zai daukaka kara a kotu ta gaba.

Tun dai bayan faruwar wannan lamari a 2022 wanda ya yi matuƙar tayar da hankalin jama’a, ɗan Chinan da aka gurfanar a gaban kotu ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kudi sama da naira miliyan 60.