✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (2)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna…

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu.  Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi.  Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne.
Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, barkanmu da ganin karshen azumin watan Ramadan lafiya. Allah Ya sa mun dace da samun duk alheran da aka kunsa a cikinsa. Lallai akwai bukatar a ga canji a halin kowanenmu da ya azumci wancan wata mai alfarma, canji ko dan yaya ne, wanda ya shafi kyautatawa a tsakanin jama’a da kuma karuwar azama wajen gudanar da ayyukan ibada. Samuwar haka tana gamsar da mu cewa lallai mun samu wani abu daga cikin alheran Ramadan.  Allah Ya ba mu dacewa da jinkanSa, amin.
Yau kuma za mu ci gaba da bayanin nau’ukan azumin nafila kamar yadda muka faro a makon jiya, wato ranar da aka yi Idin Shan Ruwa (Ranar Sallah karama). A halin yanzu dai muna kyautata zaton masu himma sun yunkura sun fara da azumin da aka fara gabatar da bayaninsa, wato Sitta Shawwal, kwanaki shida da ake yi a wannan wata na Shawwal.  In ma ba a fara ba, to kada a yi sake domin yau muna takwas ga wata ne. Mun gabatar da azumi iri uku ne, ga ci gaba:
4. Azumtar kwana uku kowane wata: Yana daga cikin nafila, idan mutum ya samu dama, ya azumci kwanaki uku a cikin kowane wata. An samo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Badadayina Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi min wasiyya da abubuwa guda uku: (1) Azumtar kwana uku cikin kowane wata; (2) Yin raka’o’i biyu na walha (hantsi) da (3) In yi wutri kafin in yi barci.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,981 da Muslim, Hadisi na 721 suka fitar da shi.
Haka nan Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada wa Abdullahi dan Amr (Allah Ya yarda da shi), a cikin wani Hadisi mai tsawo, cewa “….Kuma ka azumci kwanuka uku cikin kowane wata, saboda kowane kyakkyawan aikin ana nunka shi sau goma ne kwatankwacinsa, ka ga ke nan azuminka yana da kwatankwacin azumin shekara…” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,976 da Muslim, Hadisi na 1,159 suka fitar da shi.
An so wannan azumi ya kasance a yi shi a kwanukan haske, wato kwanakin 13 da 14  da 15 na kowane wata. Wannan kuwa saboda wani fadin Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ne, “Azumin kwana uku na kowane wata, azumin shekara ke nan, kwanakin haske, safiyar goma sha uku da sha hudu da sha biyar.” Sahihin Hadisi ne saboda hadisan da suka yi shaida a kansa, Imam Nasa’i, Hadisi na 2,419 da Abu Ya’ala, Hadisi na 7,504 da dabarani, a cikin Alkabir, mujalladi na 2, Hadisi na 2,399 daga Jabir dan Abdullah, (Allah Ya yarda da shi). Hadisin dai yana da wasu shaidu daga Abu Zarri da kattadatu dan Milhan.
5. Azumin ranakun Litinin da Alhamis: Idan an samu dama, yana da kyau a rika azumtar ranakun Litinin da Alhamis, saboda abin da aka samo daga Uwar Muminai A’isha (Allah Ya kara mata yarda), inda ta ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana hararo azumin ranakun Litinin da Alhamis.” Sahihin Hadisi ne da Imam Tirmizi, Hadisi na 751 da Nasa’i, Hadisi na 2,186; da Ibnu Majah, Hadisi na 1, 739, suka fitar.
Usamatu dan Zaidu ya tambayi Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), game da azumin ranakun Litinin da Alhamis, sai Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wadannan kwanuka ne guda biyu da ake gabatar da ayyukan bayi ga Ubangijin talikai, ni kuwa zan so a ce an gabatar da ayyukana alhalin ina cikin azumi.” Hadisi ne mai kyau (hasan) da Nasa’i, Hadisi na 2,357 da Ahmad, mujalladi na 5, Hadisi na 201 da Baihaki, a cikin Asshu’ab, Hadisi na 3,821, suka fitar.
6. Azumtar Ranar Arfa:  Yana da kyau, wanda ba ya aikin Hajji ya azumci ranar Arfa, saboda abin da aka samo daga Hadisin Abu kattada (Allah Ya yarda da shi), ya ce, ‘Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Azumin Ranar Arfa, ina fata daga Allah, ya kasance (azumtar ranar) kankara ne ga zunubin shekarar da ke gabaninta da ta bayanta.” Sahihin Hadisi ne da Imam Muslim, Hadisi na 1,162 ya fitar.
Ranar Arfa dai ita ce ranar 9 ga watan Zul Hajji!
“Shi kankarewar (zunubin) shekara biyu da aka yi magana, ko dai ana nufin cewa Allah Ta’ala Ya gafarta wa mutum zunuban shekara biyu (matukar ya nisanci kaba’irai -manyan zunubai) ko kuma Allah Ya tsare shi, a cikin shekara biyun, ba zai yi sabo a cikinsu ba.” Wannan bayani yana cikin Almajmu’u na Imam Annawawi, mujalladi na 6, shafi na 381 da waninsa.
Ba burgewa ba ne, ba mustahabbi ba ne, ga wanda yake aikin Hajji ya yi azumi a Ranar Arfa, musamman saboda shiryarwar Annabin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ta khulafa’ur rashiduna – halifofi shiryayyu, ita ce a ci abinci a Ranar Arfa, yayin da ake tsayuwar. An samo daga Uwar Muminai Maimunatu (Allah Ya yarda da ita), cewa, “Mutane sun kai kuka dangane da azumin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), a Ranar Arfa, sai ta aika masa da wata gora ta madara – alhali lokacin yana tsaye a Arfa – sai ya sha daga cikin gorar nan kuma mutane suna ganinsa.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,989 da Muslim, Hadisi na 1,124, suka fitar.
Kuma an tambayi Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), dangane da yin azumi Ranar Arfa a kuma Arfa, sai ya ce, “Na yi Hajji tare da Annabin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), amma shi bai azumce ta ba, kuma bai kasance yana umurni da azumce ta ba, kuma bai yi hani gare ta ba.” Sahihin Hadisi ne da Tirmizi, Hadisi na 751l da Annasa’i, a cikin Alkubra, Hadisi na 2,827l da Ahmad, mujalladi na 2, Hadisi na 47, suka fitar.
Abin da dai ya fi ga mahajjaci shi ne ya ci abinci a Ranar Arfa a filin Arfa don koyi da Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) da khalifofinsa da ma dai abin da yake cikinsa na fa’ida cikin cin abincin don a samu karfin tsayuwa ga yin addu’a da zikirori a cikin wannan wuri na tsayuwa. Wannan kuwa shi ne ma abin da jamhuru (mafi rinjaye) na malamai magabata suka tafi a kansa, kamar yadda bayanin haka ya fito daga Almajmu’u, mujalladi na 6, shafi na 380 da Attamhid, mujalladi na 21, shafi na 158 da Sharh Al’umda na Shaikhul Islam, mujalladi na 2, shafi na 762.  
Allah Ya ba mu dacewa, Ya tabbatar mana da bin abin da yake sunnah.  Sai mako na gaba, in Allah Ya kaddara kaiwarmu, za mu ci gaba.  
Wassalamu alaikum warahmatullah!