✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun sako dalibai da malamarsu a Kaduna

’Yan bindiga sun sako wasu dalibai da malamarsu da suka yi garkuwa da su a yankin Chikun, Jihar Kaduna. A daren Lahadi ne ’yan bindigar…

’Yan bindiga sun sako wasu dalibai da malamarsu da suka yi garkuwa da su a yankin Chikun, Jihar Kaduna.

A daren Lahadi ne ’yan bindigar suka sako malamar da dalibanta a kauyen Damba-Kasaya bayan sun karbi kudin fansa daga iyalansu.

“Sun dawo gida da misalin 8 na dare ranar Asabar bayan kusan wata biyu a hannun masu garkuwa.

“Tabbas an biya kudin fansa kafin a sako su amma ba zan fadi ko nawa ba ne”, inji wani shugaban matasan yankin Akila Luka Barde a lokacin da yake tabbatar wa Aminya an sako mutanen.

Daliban masu shekaru 15 zuwa 16 da malamarsu mai suna Christian Madugu, sun shiga mawuyacin halin ne bayan masu garkuwa sun kai har makarantarsu ta Prince Academy School hari.

A watan Satumba ne mahara suka kai harin da safe a makarantar a lokacin da dalibai ke bita gabanin fara jarabawar kammala karamar sakandare.

A lokacin harin ne ’yan bindigar sun kashe wani mai suna Benjamin Auta a kauyen.