✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zanga sun tare hanyar Legas zuwa Ibadan

Masu zanga-zanga da ke neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta SARS mai taken #EndSARS sun tare babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Tare hanyar da…

Masu zanga-zanga da ke neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta SARS mai taken #EndSARS sun tare babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Tare hanyar da masu zanga-zangar da ke dauke da kwalaye suka yi a ranar Jama’a ya haddasa cunkoso a hanyar da ta hada Jihar Legas mai iyaka da teku da sauran sassan Najeyeriya.

“Mun zo nan titin Legas-Ibadan ne saboda zanga-zangar da ake gudanarwa a fadin Najeriya domin ceto kasar.

“Baya ga #EndSARS, #Endpolicebrutality, da neman kawo karshen rashin kyakkyawan shugabanci da zalunci da ake wa matasan Najeriya, lokaci ya yi da za a ba matasa jagorancin kasar”, inji wani daga cikin masu zanga-zangar da ya ce sunansa Amaechi.

Sama da mako guda ake gudanar da zanga-zanga a sassan Najeriya inda jama’a, yawancinsu matasa ke kira da a rushe SARS wadda ake zargin jami’anta da azabtarwa da sauran nau’ika na cin zali.

A ranar Lahadi Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya sanar da rushe SARS kafin daga bisani ya sanar da kirkirar SWAT a matsayin rundunar da za ta maye gurbinta.

Ya yi wa dukkannin jami’an SARS kiranye, yana mai cewa za a sauya musu wararen aiki bayan an yi musu gwajin lafiya da na kwakwalwa an kuma sake ba su horo tare da sauya musu tunani.

A cewarsa, jami’an SWAT ma za a yi musu irin wadannan gwaje-gwaje sannan a ba su horo na musamman kuma za a kafa kwamitin hadin gwiwa da zai rika lura da ayyukansu da kuma binciken zargin cin zali.

Duk da haka masu zanga-zangar ba su gamsu ba, inda suka kara da mika ga Gwamnatin Tarayya wasu bukatu biyar wadanda gwamnatin ta amince da su a ranar Talata.

Bukatun sun hada da yi wa jami’an SARS gwajin kwakwalwa, kara wa ‘yan sanda albashi, hukunta wadanda suka ci zarafin jama’a da kuma biyan diyya ga iyalan masu zanga-zanga da aka kashe.

Zuwa yanzu kwana uku ke nan da gwamanti ta sanar da amicewa da bukatun amma masu zanga-zangar sun ci gaba inda suke nuna rashin yarda da alkawarin gwamnatin wanda suka ce ta fatar baki ce kawai.