✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke matar da ta kashe ’ya’yanta 2 a Kano

An cafko matar ne bayan ta tsere jim kadan da ta kashe ’ya’yan nata biyu

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama matar da ake zargi da yi kashe ’ya’yanta biyu a Kano.

A ranar Asabar ne rahotanni suka ce matar mai suna Hauwa Habibu mai zama unguwar Diso a Karamar Hukumar Gwale cikin birnin Kano ta cika wandonta da iska bayan ta yanka ’ya’yan saboda kishiyar da minjinta ya yi mata.

Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa ’yan jarida a Kano ranar Lahadi.

Ya ce a ranar Asabar rundunar ta sami rahoton cewa matar ta yi wa yaran nata biyu, Yusuf Ibrahim mai shekara shida da kuma Zahra’u Ibrahim mai shekara uku yankan rago.

Kiyawa ya ce, “Da samun labarin muka aike da dakarunmu inda muka iske yaran a mace”.

Ya ce daga nan ne aka garzaya da su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda likitoci suka tabbatar sun mutu.

Ya kuma ce matar ta yanki wata kanwarta mai suna Aisha Abdullahi mai shekara 10 da adda wacce ita kuma aka kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Habu Sani, ya bayar da umarnin a mayar da binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin fadada bincike.