✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa ku koyi sana’a don sama wa kanku mafita – Dan Iyan Jama’a

Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Kaduna, Kwamared Sanusi Maikudi ya shawarci matasan jihar su yi watsi da girman kai; su tashi su koyi sana’o’i kafin…

Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Kaduna, Kwamared Sanusi Maikudi ya shawarci matasan jihar su yi watsi da girman kai; su tashi su koyi sana’o’i kafin dole ta sa su ta hanyar rasa wadanda suka dogara da su a rayuwarsu.

Kwamared Sanusi, ya yi kiran ne a wajen taron shekara-shekara na Kungiyar Dalibai ’Yan Asalin Masarautar Jama’a (JESA) da ke manyan makarantun kasar nan ta gudanar.

Kwamared Sanusi, wanda shi ne Dan Iyan Jama’a, ya ce dukkan fitattun masu kudin duniya ’yan kasuwa ne masu dogaro da kansu; wadanda suka jajirce a rayuwarsu har Allah Ya kawo su matsayin da suke kai.

“A matsayinku na matasa bai kamata ku tsaya jiran sai kun mallaki shaidar karatu iri kaza kun samu aikin gwamnati kaza ba; domin hakan kuna bata lokacinku ne kawai. Da kun san alherin da ke cikin kasuwanci da sana’o’i da ba ku tsaya jiran ayyukan gwamnati ba,” inji shi

Kwamared Sanusi ya kara da cewa: “Dan kasuwa ko mai wata sana’a ba kansa kawai yake taimakawa ba; domin idan ya bunkasa zai debi ma’aikata, wadanda ta haka ya rage musu zaman banza a cikin al’umma sannan gwamnati za ta amfana da shi domin za ta rika zuwa karbar haraji a hannunsa.”

Dan Iyan Jama’a ya bayyana takaici kan yadda al’ummar yanzu take asarar abubuwa da yawa da ’yan baya suka amfana da su, inda ya ce ’ya’yan malamai ba su zamowa malamai kamar yadda ’ya’yan masu kudi suke talaucewa duk a sanadiyyar girman kai da rashin tashi tsaye don su mallaki na kansu.

“Idan mutum ya ki yi wa kansa kiyamullaili; ko da matar aure ce a cikin gidanta da ba ta sana’a to da zarar mutum ya rasa mai yi masa sai ya koma kame-kame a rayuwarsa; wanda hakan ke taimakawa wajen samar da ayyukan assha a cikin al’umma,” inji shi.

Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, wanda dansa Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Sadik Muhammad, ya wakilta, ya nuna godiyarsa kan yadda kungiyar ke shirya wa dalibai da sauran matasa taron wayar da kai kan fannonin rayuwa daban-daban.

Da yake nasa jawabi, Dokta Muhammad Kabir ya yi kira ga matasa maza da mata da kada su raina sana’a kowace iri ce; kuma komai kankartarta, sannan su zamo masu lissafi tare da juriya a sana’ar don tsallake duk wani kalubale da za su fuskanta.

Dokta Kabir, ya ce  addinin Musulunci ya karfafa neman na kai; domin samun rufin asiri a duniya da kuma tsira a Lahira, inda ya yi kira a gare su da su tsaya kan neman halaliya kawai.

Maza da mata ne daga makarantu daban-daban da suka hada da jami’o’in ABU, Zariya da BUK, Kano da KASU, Kaduna da makarantun kiwon lafiya na Makarfi da Kafanchan da Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya suka halarci taron, inda aka rantsar da sababbin shugabannin da za su ja ragamar kungiyar.

Bikin wanda aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata ya hada shi da bayar da kyaututtuka ga wadansu fitattun mutane a Masarautar Jama’a da suka bayar da gudunmawarsu a fannoni daban-daban kuma an gudanar da shi ne a dakin taro na Dubu Ebent da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna.

Wadanda aka karrama sun hada da Mai martaba Sarkin Jama’a da Talban Jama’a Alhaji Sa’idu Adamu da Dan Iyan Jama’a Sanusi Maikudi da Malam Aminu Nababa Tahir da sauransu.