✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na biya tarar N10,000 saboda ban saka takunkumi ba —Shaikh Rigachikun

‎Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatis Sunnah ta kasa mai Hedkwata a Jos, Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya bayyana yadda aka ci…

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatis Sunnah ta kasa mai Hedkwata a Jos, Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya bayyana yadda aka ci shi tarar N10,000 saboda bai saka takunkumin fuska ba.

Aminiya ta samu rahoton cewa hakan ya auku ne a makon jiya lokacin da Shaikh Sambo ya ziyarci wani abokinsa a unguwar Rimi cikin Kaduna domin jajanta masa rasuwar mahaifiyarsa.

Shaikh Sambo, wanda shi ne ‎kuma shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Kaduna, ya ce shi mutum ne da ba ya karya dokar gwamnati don haka da wuya ya fita ba tare da ya saka takunkumin fuskar ba, sai a wannan rana da ya ajiye a cikin motarsa bayan ya fito daga gidan rediyon jiha inda aka gayyace shi wani shiri.

“Gaskiya ne an kama ni a kotun tafi-da-gidanka da ke bibiyar wadanda ba su saka takunkumi a fuskarsu ba.

‘Na je ta’aziyya ne’

“Abin da ya faru, akwai gidan talabijin na Kaduna ta suka gayyace ni wani shiri da karfe 8:00 na safe.

“Kusan karfe 8.00 din ina wajen bayan Allah ya nufa na kammala shirin akwai wani dan uwa da ake ce mai Alhaji Ado Fara da mahaifiyarsa ta rasu a Kano sai na ga kamata ya yi tun da na shigo cikin Garin Kaduna na je na yi masa ta’aziya.

“Da na idar da ta’aziyar sai na yi nufin in biyo ta Unguwar Rimi in dawo gida. To ina zuwa daidai babban titin da ake zuwa Jami’ar Kaduna sai na iske ’yan sanda a tsaitsaye.

“Wannan takunkumi na ajiye shi a mota tun da ni ba dabi’ata ba ne in fita babu shi.

“To sai dan sandan nan ya tsayar da mu sai ya ce in yi can ana san ganinmu, ina zuwa a mota sai na iske wata majistare a wajen wacce ke jagorantar zaman.

“Kuma ina zuwa na ganta, sai ta ce min an kama mu ne domin ba mu saka takunkumin rufe fuska ba, sai na ce eh gaskiya ne.

“Da ni da wani yarona Shuaib, sai na ce mata a ka’ida meye abin yi sai ta ce min tara za a yi mana dubu biyar – biyar ni da shi. Sai na ce ta rubuta rasidi a ba ni.

“Na saka hannu a cikin aljihuna na dauko 10,000 na ba su, na ce a rubuta mana rasidi daban-daban.

“Bayan an ba mu shi ne suke kokarin su yi min bayanin cewa doka ce sai na ce ai babu komai, kowa lokacin shi yake amfani da shi”, inji Shaikh Sambo.

‘Abin da ya kamata’

Sai dai ga alama wannan lamari bai yi wa malamin dadi ba, duk da ya amince cewa bai saka takunkumin ba kamar yadda aka tuhume shi.

“Kamar yadda na fadi ni ba al’adata ba ce karya dokar gwamnati domin malaman addini muke cewa a kiyaye tsari amma ni abin da na fahimta tun da gwargwadon tsari ina da fahimtar shari’a domin abin da na karanta ke nan, a ka’ida kuma a fahimtata ba daidai ba ne a kakaba wa mutane wannan dokar ba tare da an kai majalisa an tattauna ba.

“A tattauna a sanar da ’yan jihar Kaduna su san cewa an samar da dokar sannan a zartar.

“Yanzu wannan siyasar da ake mana da sunan demokradiya mulkin kama karya ake mana,” inji shi.

Wajibcin saka takunkumin rufe fuska a duk lokacin da za a fita dai ya fara aiki ne da jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya, wanda a ciki ya bayyana janye dokar zaman gida sannu a hankali a jihohin Legas da Ogun da ma Yankin Babban Birnin Tarayya.

A jawabin ne dai shugaban kasar ya ayyana wasu matakai da za a bi a fadin kasar don hana coronavirus yaduwa, ciki gar da amfani da takunkumin.

Jim kadan bayan jawabin ne kuma ya rattaba hannu a kan dokar yaki da COVID-19 wadda ta tabbatar da hakan.