✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAHCON ta fito da ka’idojin tafiya Umrah daga Nijeriya

Hukumar kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta fitar da sharuda da ka’idojin da maniyyata Umrah za su cika kafin su samu amincewar tafiya…

Hukumar kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta fitar da sharuda da ka’idojin da maniyyata Umrah za su cika kafin su samu amincewar tafiya aikin ibadar a Kasa Mai Tsarki.

Dokokin da NAHCON ta fitar ta shafinta na Facebook su ne kamar haka:

  1. Matafiyi ya kasance daga shekara 18 zuwa 50
  1. Nuna takardar shaida daga amintaccen wurin gwaji cewa ba ya dauke da cutar coronavirus.
  2. Kar wuce sa’a 72 daga lokacin gwajin kafin tashi daga filin jirgin sama zuwa kasar Saudiyya.
  3. Kiyaye ka’idojin neman izinin ziyara zuwa Masallacin Annabi (S.A.W) da zuwa addu’a Rawdha kamar yadda aka gindaya.
  4. Shaidar amincewar ranar tafiya da dawowa.
  5. Killace kai na tsawon kwana uku a masauki kafin fara gabatar da aikin Umrah.
  6. Samun abun hawan zirga-zirga daga filin jirgi zuwa masauki.
  7. Samun abun hawa domin zirga-zirga daga masauki zuwa Harami da Mikati.